September 17, 2026

Kotu Ta Samu Shugaban Kamfen Peter Obi, Doyin Okupe Da Laifin Halatta Kuɗin Haram.

0

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu shugaban yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, Doyin Okupe, da laifin halatta kuɗin haram.

Idan zaku iya tunawa, hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ta EFCC, ta gurfanar da Okupe a shekarar 2019 gaban kotu kan tuhume-tuhume 59 da suka shafi karkatar da kudade da suka kai naira miliyan 702.

An dai gurfanar da Okupe a gaban mai shara’a Ijeoma Ojukwu, tare da kamfanoni biyu masu suna – Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *