Kotu Ta Hana Majalisar Jihar Oyo Tsige Mataimakin Gwamna.
Babbar kotun jihar Oyo ta umarci ‘yan majalisar dokokin jihar da su dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan.
Makonni biyu da suka gabata, majalisar dokokin jihar ta aika da sanarwar tsige mataimakin gwamnan bisa zargin watanda da kudi, yin watsi da aikin ofis, rashin biyayya da dai sauransu.
Rauf Olaniyan ya shigar da karar ne a ranar Talata, 28 ga watan Yunin shekarar 2022, inda yake kalubalantar batun tsige shi.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Ladiran ya umarci ‘yan majalisar dokokin jihar da su ci gaba da mutumta juna, wanda hakan ya hana ‘yan majalisar dokokin jihar daukar matakai na ci gaba da yunkurin tsige shin.
Tun da farko, lauyan wanda ya shigar da kara Afolabi Fashanu (SAN) ya bukaci kotun da ta amince da bukatarsa ta hana majalisar dokokin jihar Oyon daukar mataki kan tsige mataimakin gwamnan.
A bukatar da lauyan wanda ake karar A. A Olabiyi ya gabatar, ya bukaci kotun da ta ba shi lokaci domin ya amsa bukatar mai karar, inda ya ce an sanar da matakin farko a ranar Talata, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman kotun, Fashanu ya ce, “Mun shigar da kararraki guda biyu, amma kotun ta ba da umarnin wucin gadi na hana majalisar dokokin jihar yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan.
Sai dai mai shari’a Akintola ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Talata 5 ga watan Yuli 2022 domin ci gaba da sauraren karar, tare da baiwa lauyan majalisar damar amsa yadda ya kamata kan lamarin.
