September 18, 2026

Kotu Ta Daure Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’a Shekaru 35 Kan Kadakalar N260m A Najeriya.

0

Wata babbar kotun birnin tarayya da ke Garki Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Maryam Hassan Aliyu ta samu Farfesa Magaji Garba tsohon shugaban jami’ar tarayya ta Gusau da laifuka biyar da suka hada da karbar kudi ta hanyar karya da yin takardun jabu, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 35 a gidan yari, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.

Hukumar da ke bankado masu yima tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ce ta samu wannan nasarar a gaban kotu ranar Alhamis.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Garba a gaban kotu a ranar 12 ga Oktoba, 2021, bisa zarginsa da karbar wasu kudade daga hannun wani dan kwangila don ba shi kwangilar Naira biliyan 3 na bangon Jami’ar.

Laifin ya sabawa sashe na 1 (1) (a) kuma hukuncinsa a karkashin sashe na 1 (3) na damfarar wanda la fara amsar kudinshi da sauran Laifukan da ke da alaka da zamba na shekarar 2006.

Saidai yaƙi amsa laifukan da ake tuhumarsa da su, dalilin da yasa aka ci gaba da gudanar da shari’ar.

Bayan kiran shedu tare da gabatar da takardun hujja masu yawa, EFCC ta rufe karar ta a ranar 14 ga Disamba, 2021.

Da yake yanke hukunci a jiya Alhamis, alkalin kotun ya ce kotun ta gamsu cewa yana da laifi ba tare da wata shakka ba.

Ya bayyana wanda ake karar da cewa “mai laifi ne” akan tuhume-tuhume biyar da ake masa, sannan kuma ya yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai akan tuhuma ta 1-3 ba tare da zabin biyan tara ba, da kuma daurin shekaru bakwai a gidan yari akan tuhume-tuhume na 4 da 5, tare da zabin biyan tarar Naira miliyan 10 akan kowannensu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *