Kotu a Zamfara Taba Kwamishinan Gona wa’adin Kwana Biyu Da Ya Dawo Da Tarakta 58 Da Ya Saida
Daga Hussaini Ibrahim
Babbar Kotun daukaka Kara ta biyu ta jihar Zamfara,wace Mai shaari’a Bello Shinkafi kewa jagoranci ya ba Kwamishinan Ma’aikatar Gona Umarnin Kwana biyu da ya dawo da Taraktoci 58 ,da Aya ake zargin ya sauda agabanta .dan biyan Kamfanin Dunbulun Investment hakin sa da ya ke bin Gwamnatin Jihar ta Zamfara.
Barista Musbahu Salahudini wanda ya ke kare Kwamfamin Dunbulum, yayi wa manema labarai karin bayani akan hukuncin Kotun kamar haka, a shekara ta 2019 ,Kotun daukaka Kara ta Uku tayi hukuncin tsakanin Gwamnatin Jihar Zamfara zata biya Kamfanin Dunbulun Investment kudi naira miliyan Dari biyu da Sharin , alokacin Gwamnatin ta biya miliyan Dari da Yan Kai saura miliyan Dari da uku suka rage bata biya ba,sai babbar Kotun ta uku ta bada Umarni kama kaddarurin Gwamnatin alokacin ta kama wasu motocin Gwamnatin da Taraktoci Ma’aikatar Gona 58 ,a cikin watan Disanba na bara da nifin ayi gwanjan motocin dan abiya Kamfanin Dunbulun kidin sa sai Kotun tayi ta jankafa .akan batun saida kaddarurin.Inji Barista Musbahu.
‘Barista Misbahu ya ƙara da cewa, Dokar taba Mai Kara dama idan alkalin da ke shiri’a ba zayyimaka adalciba to ka kai kara ga Kotun gaba wannan ne ya bamu damar kai karar ga Kutun daukaka kara ta 2 ,dan neman hakin mu .kuma mun shigar da Kara akan Kotun ne dan tilastawa Kotu da 3 tayi gwanjan kayan Dan biyan mu hakokin mu sai muka samu labarin cewa, Kwamishinan gona ya Kwashe Taraktocin 58 ya saida.
Ya ce ,akan haka ne suka shigar da kara dan shedawa Mai shaari’a Bello Shinkafi na Kotun daukaka Kara ta biyu agabn Lauyan Gwamnatin akai wani bai musaba,sai Mai shaari’a Bello Shinkafi ya amsa kokenmu na Kwamishinan gona da ya gaggauta kawo Taraktoci 58 ,cikin kwana biyu kuma ya mika kansa a gaban Kotun a ranar 14/9/2022, ya kare kansa akan wasa da shiri’a da yayi Motoci na gaban Kotun ya zai kwashe ya saida .inji Barista Misbahu Salahudini.
‘Yan jaridu sun nemi jin tabakin Lauyan Gwamnati Jihar Zamfara,ya bayyana masu cewa,maida hurimin yin magana da ‘Yan jaridu sai da Umarni Kwamishinan shari’a na Jihar.
