September 17, 2026

Kisan Ɗan Jarida: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Sa Kaimi Wajan Gudanar Da Cikakken Bincike A Zamfara

0

Daga Hussaini Ibrahim

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayar da tabbacin gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa wani gogaggen dan jarida, Hamisu Danjibga.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Yazid Abubakar ya fitar a Gusau.

A cewar sa, ASP Yazid Danjibga, wanda shi ne wakilin Sashen Hausa na Muryar Najeriya (VON) na jihar ya bace tsawon kwanaki uku kafin a tsinci gawarsa a wani rami a bayan gidansa a ranar Laraba.

ASP ya kara da cewa,rundunar ta samu bayanai game da bacewar dan jaridar, wanda wakilin Sashen Hausa na Muryar Najeriya (VON) ne, daga shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) Ibrahim Musa.

A cewarsa, dan jaridar ya bace tun ranar Lahadi, 16 ga watan Satumba.

“Bayan samun labarin, jami’in ‘yan sanda yanki Tudun-Wada da ke Gusau, babban birnin jihar ya sanya tawagar jami’an tsaro domin su binciki lamarin.

“Da misalin karfe 1:33 na rana, ranar 20 ga watan Satumba,aka tsinci gawar dan jaridan wani rami masai a bayan gidan marigayin.”

Ya kara da cewa matakin ya kuma yi sanadin kama wani mutum da ake zargi mai suna Mansur Haruna mai shekaru 35 da wata wayar Gionee da ake zargin ta marigayin ne.

“Rundunar ‘yan sanda a karkashin kwamishinan ‘yan sanda, Muhammad Dalijan, tana mika ta’aziyya ga iyalai da mambobin kungiyar NUJ, hukumar gudanarwar Sashen Hausa na VON da kuma daukacin alumar jihar bisa rasuwar dan jaridan.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *