Katsina Na Neman Shugaba Irin Marigayi Umaru Musa Yar’adua. Cewar Dakta Rabe Darma
Tsohon shugaban Asusun PTDF injiniya Mutaqqa Rabe Darma ya bayyana cewa jihar Katsina Na bukatar shugaba irin marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua saboda kudirin sa na inganta tattalin arziki da tallafawa matasa.

Injiniya Mutaqqa Rabe ya yi wannan bayani a lokacin da yake gabatar da ƙasida akan rayuwar marigayi Umaru Musa Yar’adua da ya cika shekaru sha uku da rasuwa a ɗakin taro na jami’ar Umaru Musa da ke Katsina.
Taron wanda wata kungiya mai sa ido akan al’amuran shuwagabannin ta shirin ya samu halartar ‘yan uwa abokan arziki da masoya da kuma magoya baya.
Injiniya Mutaqqa Rabe ya cigaba da cewa tsohon shugaban Kasar ya kawo kudirori da dama da zasu taimaki rayuwar matasa a wancan lokaci saboda su damu kyakkyawar makoma
“Irin abubuwan da marigayi Umaru Musa Yar’adua ya bari za a dade ba a manta da su ba, sannan ba za a taɓa mantawa da irin gudunmawar da ya bada ba don ganin matasa ba su shiga wani hali ba,” inji shi
Haka kuma ya cigaba da cewa yana fatan gwamnati mai zuwa ta yi koyi sannan ta ɗauki sakon mulki irin na Umaru Musa domin ta hake ne kawai al’umma za su samu cigaba.
Kazalika Injiniya Mutaqqa Rabe ya yi fatan cewa nan gaba kaɗan za a samu aminci da yarda da juna tsakanin shuwagabannin da mabiya inda ya ce ta haka za a kafa harsashin cigaba da zaman lafiya.
Shima da yake nasa jawabin Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga ya ce tsohon shugaban Kasa Umaru Musa Yar’adua yana cikin mutanen da yake ganin ƙimarsu musamman ta fuskar ɗora harsashin ilimi musamman idan aka kwantanta shi da sauran gwamnoni.
Farfesa Sani Abubakar Lugga ya cigaba da cewa ya tuna lokacin da marigayi ya zo da sabon salon maida makarantu firamare na zamani domin su yi gogayya da sauran jihohi a wancan lokaci.
Daga karshe Farfesa Sani Abubakar Lugga ya yi kira da fatan cewa shuwagabannin yanzu za suyi koyi da irin halayen tsohon shugaban Kasa Umaru Musa Yar’adua.
