September 19, 2026

Buhari Ya Rantsar Da Arase A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Ayyukan Yan Sandan Najeriya.

0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon shugaban hukumar kula da ayyukan yan sanda, wato tsohon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Solomon Arase (mai ritaya).

Arase ya amshi rantsuwar kama aiki da misalin karfe 10:05 na safiyar yau Laraba 29/03/2023 a dakin taro na fadar shugaban ƙasa dake Abuja a gaban shugaban ƙasa Buhari, mataimakin shi Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Ibrahim Gambari, da sauran membobin majalisar shugaban kasa.

Idan za a iya tunawa majalisar dattawan Najeriya ce ta tabbatar da Arase a matsayin shugaban hukumar.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kasar ya mika sunansa a ranar 24 ga watan Junairu, 2023, inda ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da shi kamar yadda sashe na 153 (1) da na 154 (1) na kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Arase, mai shekaru 65, wanda ya yi ritaya a shekarar 2016, shi ne Sufeto-Janar na ‘yan sanda na 18th (tsakanin Afrilu 2015 da Yuni 2016) kuma ya yi aiki a wurare daban-daban ciki har da shugaban hukumar leken asiri da binciken manyan laifuka, sashen tattara bayanan sirri na farko na ‘yan sandan Najeriya.

Shugaban ya kuma rantsar da mambobin hukumar kula da da’ar ma’aikata biyar.

Membobin sun haɗa da Murtala Kankia daga jihar Katsina (Arewa-maso-Yamma); Zephaniah Bulus daga Jihar Nasarawa (Arewa Ta Tsakiya) da Farouk Umar daga Jihar Yobe (Arewa Maso Gabas) da Taofeek Abdulsalam daga Jihar Ondo (Kudu maso Yamma) da Farfesa Juwaria Badamasi daga Jihar Kogi (Arewa Ta Tsakiya).

A halin da ake ciki kuma, Arase ya yi alkawarin ba da fifiko ga jin dadin ƙanana da manyan jami’ai rundunar ‘yan sandan Najeriya.

A wata hira da yayi da manema labarai na fadar shugaban kasa, ya yi alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma matsalolin da ke faruwa tsakanin babban sufeton yan sanda da hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan.

“Za mu tabbatar da ganin mun ci gaba da sanya kwarewarmu ta cikin gida da ta kasashen waje a cikin aikin inji Arase, a cewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *