Karancin Sabbin Kuɗi: CBN Ya Je Injinan ATM Domin Hukunta Bankunan Dake Zuba Tsaffin Kuɗi.
Yayin da jama’a ke ci gaba da nuna bacin ransu dangane da karancin sabbin takardun kudin Naira, a wannan Alhamis ɗin babban bankin Najeriya (CBN) ya kai samame na’urorin ATM na bankuna daban-daban domin tabbatar da matakin da ake bi wajen raba takardun kudin Naira da aka sake fasalinsu.
Abin da ya ba ma’aikatan CBN mamaki shi ne yadda tsofaffin takardun kudaden suka yi ta fitowa daga galibin na’urorin ATM na bankuna a lokacin samamen.
Wasu rumfunan ATM ne dai kaɗai ke bada sabbin takardun kudin na Naira, abinda babban bankin ya ce sam ba za a amince da shi ba.
Da yake magana bayan kammala ziyarar, Daraktan bakin CBN kuma Manajan Darakta na Bankin bada rance na NIRSAL Abdullahi Kure, ya ce za a ci gaba da sa ido a kan bankunan, yana mai jaddada cewa wadanda aka samu da laifin tarawa da karkatar da sabbin takardun kudaden za a hukunta su.
Ya ce: “Muna yin bincike don sanin wadanda ke samun sabbin takardun kudi da abin da suke bayarwa ko kuma dalilin da ya sa ba sa fitar da su. Muna sa ido don sanin ko bankunan suna tarawa, karkatar da su ko kuma ba su karɓi sabon kuɗin ba.
A kan yiwuwar tsawaita wa’adin, ya ce “ba zan iya cewa komai ba”.
Ya kara da cewa, an baza manyan Daraktocin CBN a fadin kasar nan domin zurfafa wayar da kan mutane akan sabbin takardun kudin na naira.
Ya kara da bayyana cewa, babban bankin yana tuntubar malaman addini da sarakunan gargajiya don ganin sun samu nasarar shirin.
Na’urorin ATM din da suka ziyarta sun haɗa dana GCO, Access Bank da kuma Keystone Bank dake a unguwar Wuse a Abuja.
Saidai a bankin Access dake Wuse, Manajan Ayyuka, Ugo Chinenye, ya musanta ajiyar sabbin takardun kuɗin, inda ya bayyana cewa bankin na lode Injinan ATM din shi da adadin sabbin takardun kudaden da yake karba daga babban bankin.
A fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi Adamu Baba Yunusa, Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya a Babban Birnin Tarayya sun yi kira da a kara wa’adin ranar rufe amsar takardun kudaden ta 31 ga watan Janairu domin ba da damar wayar da kan jama’a musamman a matakin karkara, a cewar majiyar Popular News Hausa ta Sunnews.
