September 19, 2026

Jihar Akwa Ibom Ta Gurfanar Da Wasu Yan kasar China 2 Kan Hayaki Mai Guba.

0

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta tabbatar da gurfanar da wasu ‘yan kasar China biyu da aka kama, tare da tsare su watannin baya bisa zargin gurbata muhalli da hayakin masana’antu wanda ya saba wa dokar kare muhalli ta jihar.

Wadanda ake tuhumar sun hada Manajan Darakta Peter Yuan da kuma manajan tallace-tallacen kamfanin Golden Tripod Int’l Ltd, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership.

A cewar kwamishinan muhalli da ma’adanai na jihar Charles Udoh, ana tuhumar su ne da laifuffuka da dama, wadanda suka hada da “gurbacewar muhalli, hana jami’an gwamnati dake bakin aiki, takurawa jama’a da hayaƙi da kuma kwace motocin gwamnati a lokacin bincike”.

Udoh, wanda ya yi wa manema labarai karin bayani a jiya, ya ce kamfanin, ya mamaye tsohon harabar cocin Solid Rock Kingdom dake unguwar Ikot Ebido Oku daura da titin Ikot Ekpene, Uyo, babban birnin jihar, inda ya ce ya yi ta aiki ba bisa ka’ida ba tsawon wasu ‘yan shekaru, ba tare da samun izinin aiki, ta haraji da kuma tsarin kula da ma’aikatar muhalli ba.

Ya tunato cewa ma’aikatar muhalli tare da hadin gwiwar kwamitin majalisar dokokin jihar mai kula da muhalli, da hukumar kula da sharar ta jihar sun ziyarci kamfanin a sati biyu da suka gabata, inda daga bisani suka ba da umarnin dakatar da ayyukan kamfanin.

Ya ce, “mazaunan wurin sun aiko masu da takardar koke, kuma ya tura jami’an kiwon lafiyar su na muhalli su je su duba, sun je su duba aka hana su. Bayan haka, sun ba su sanarwar rage aiki, amma dai shiru.

Ya ce, “A lokaci guda kuma, shugaban majalisar, kwamitin majalisar kan muhalli shi ma ya kira don tattaunawa kan karar. Sun gayyaci kamfanin, ya yi watsi da su tare da aiki lauya da zao yi magana a madadin kamfanin. Sun sake gayyatar kamfanin karo na biyu, ya sake aiko wani lauyan da zai magana a madadin su. Ya ce a wannan lokacin, dole ne suka hada hannu da hukumar kula da muhalli.

Ya ce “ da suka isa ya gabatar da kan shi sai mutanen suka kulle masu gate. Amma da suka samu sa’ar da kan su, sun sha mamaki. Matasan dake aiki wurin ma rayuwar su na fuskantar baraza na tsawon shekaru.

Ya ce “ mutanen na aikin narkar da aluminum ba tare da kayan kariya ba, suna kaurin aluminium, ga kuma dagwalon ruwan kamfanin da suke fitarwa.”

Ya ce “ya nemi ganin ma’aikatan, da farko, wasu ‘yan kasar China biyu suka fito. Ya ce, “ina takardar amincewar hukumar kula da muhalli?, ba a samu ba. Daga nan sai suka umarci matasan dake wurin su ci gaba da jifar su da duwatsu.

“Sai direban shugaban kwamitin majalisar kan muhalli ya kyale motarsa ya gudu”.

“Kuma duk da sun je wurin da tawagar ‘yan sanda, sai da suka matsa don hana su. Suka kai rahoto ga gwamnan da ya ba da umarnin a kai karar, saboda haka suka shigar da kara.”

“An tsare su gidan yari, daga baya kuma aka gurfanar da su a gaban kotu bisa zarge-zarge uku da suka hada da gurbata muhalli, hana jami’an gwamnati aikinsu da kuma kai hari kan jami’an gwamnati, da kuma kwace motar jami’an.

Ya ce “suna bukatar ganin takardun basu izinin aiki dana biyan haraji, hadi dama sauran takardun da suka wajaba.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *