Jam’iyyar NNPP Ta Yi Sabbin Shugabanni A Jihar Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Jam’iyyar NNPP ta gudanar da zaben Shuwaganinta da za su ja ragamar shugabancin jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa a jihar Katsina.
Sabon sakataren jam’iyyar na jiha, Dakta Sani Umar Kankia ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina inda ya ƙara da cewa Alhaji Gambo Salisu shi ne sabon shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Katsina
Ya ƙara da cewa an sanya shugabancin jam’iyyar a shiyyar Katsina, sai kuma sakatare a shiyyar Daura ya yin da aka sanya ma’ajin jam’iyyar a shiyyar Funtua.
“Haka kuma muna da mataimakan shuwaganinta guda uku daga kowace shiyya wanda bisa haka ne suka samu fahimtar juna wanda aka gudanar da zaɓe babu hamayya.” Inji shi
Sai dai kuma ya ce baban abinda ya kawo su wajan wannan taro shi ne su ƙara tabbatar da shugabancin da aka riga aka samar ta hanyar maslaha (consunssor) wanda ya ce dukkanin magoya bayan jam’iyyar NNPP sun zo domin su gaisa da juna sannan su sada zumunci.
Da yake jawabi shugaban riko na jam’iyyar NNPP Alhaji Hadi Mai-Dawa ya ce duk wasu shirye-shirye sun riga sun kammala domin samun nasarar Jam’iyyar a Ƙasa baki ɗaya.
Haka kuma ya ƙara jadadda irin karfin da jam’iyyar ke da shi a ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina, sannan ya nuna fatan da suke da shi na samun nasara daga ɓangaren su.
Sannan ya bayyana cewa baban gurin wannan jam’iyya shi ne ta tabbatar ta kawo canji mai ma’ana da cigaba a jihar Katsina da kuma ƙasa baki ɗaya.
