Jam’iyyar APC Ta Haramta Zuwa Da Makamai Lokacin Yakin Neman Zaɓe a A Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim
Shugaban Kwamitin Yada labarai na yakin neman zaben jam’iyyar APC da za’afa a gobe Talata, Hon Ibrahim Ɗanmalikin Gidan Goga ya tabbatar da hana yawo da makamai a lokutan yakin neman zaben ga matasa ‘yan jami’yyar APC a faɗin Jihar ta Zamfara.
Ɗanmalikin Gidan Goga ya bayyana haka a taron manema labarai da Kwamitin yayi a dakin taron gidan rediyon jihar Zamfara.
Kwamitin ya tabbatar da cewa, wata jama’iyyar adawa bata taba cin zabe a jihar Zamfara ba,ko da wasu gwamnoni da suka sauya sheka a shekarun baya suka koma wata jam’iyyar sundawo gidan na gaskiya watau jam’iyyar APC itace ke mulkin jihar Zamfara.inji Ɗanmalikin Gidan Goga.
” Dan haka wanda keda nasara baya yawo da makami ,dan duk wanda aka kama da makami ko cin abu sana’ar wani baibiyaba , lallalai zai gamu da fushin Jami’an Tsaro .
Akan haka ne kuke kira da dabbar murya a lakutan kamfen da za’a Fara gobe Talata a Kauran Namoda, Laraba a Bakura da ranar Alhamis a Bungudo da Jama’a su koyaye bindoka da oda.inji Hon Ibrahim Danmalikin Gidan Goga.
