Jami’ar Tarayya Ta Gusau Ta Kori Ɗalibai 7 Ta Dakatar 6
Daga Hussaini Ibrahim
Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta kori dalibai bakwai tare da dakatar da Ɗalibai 6 bisa aikata laifukan da suka saba wa ka’idojin makarantar.
Jami’in yada labarai na Jami’ar Umar Usman, ya ne bayyana haka a takardar da sanyawa hannu ga manaima labari a Gusau.
Acewar ɗaliban da abin ya shafa an kama su ne da laifuka da dama da suka saba wa doka da ka’idojin jami’ar.
Umar Usman ya kara da cewa “binciken kwamitin da rahotan da suka bada akan na tababtar laifukan su ya ba Jami’ar kwarin gyuwar hukunta su.”.
” laifukan da daliban suka aikata sun hada da Sata da cin zarafi, a kafafen sada zumunta da kuma satar jarabawa jarrabawa.
“Mu’awiyya Bello, magatakarda na Jami’ar, da Yakubu Audu suka gabatar da korar daliban.”
Daliban da aka kora sun hada da Daniel Ibeh Mayowa na sashen ( Educational Foundation ), Habibu Abdul, (Microbiology), Abdulsalam, Abubakar ( Microbiology), Faruk Alayande Olamilekam,( Educational Foundation) da Iortim Philemon Vasue na Sashen Kimiyyar Siyasa.
Sauran sun hada da Abubakar M. Lawal, sashen kula da harkokin kasuwanci da James Joseph, mai kula da harkokin kasuwanci.
Daliban shida da zasu maimaita zango biyu na Karatun su, su ne Emmanuel Chibuzor Ejikeme na Ilimin Kimiyya, Idowu Ojo Oni, (Educational Foundation) da Khadija Abdulrahman Bala (Plant Science and Biotech).
Sauran Daliban da zasu maimaita zango daya sun hada da Sadiya Sani Garba,( Plant Science and Biotech),Balkisu Bello, (Plant Science and Biotech ) da Ibrahim Mu’azu Lawal, Kimiyyar Siyasa.
A cewar Umar, wadannan laifuka ne da suka saba wa tanadin tsarin dokar Jami’ar sashe na A, abu (xxv), shafi na 62; Shafi na 68, abu (iv) akan Dokokin Gudanar da ka’idodin ɗalibai; da Sashe L, Shafi na 69-73, abu (i – xxv) na Jagoran ɗalibai.
