Idan Na Zama Shugaban Ƙasa Zan Samar Da Tsaro A Jihar Katsina – Udon Emmanuel
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar PDP kuma gwamnan jihar Akwai Ibom Dakta Udon Emmanuel ya ce bayyana cewa idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasa aikin samar da tsaro zai fara yi a jihar Katsina.
Gwamna Udon Emmanuel ya furta haka a lokacin da ya kawo ziyarar neman kuriar masu zaɓan fidda gwani a zaɓan da za a gudanar na shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar PDP.
Haka kuma ya ƙara da cewa abubuwa a Najeriya sun koma baya so sai saboda haka ya ne domin ya ce ci Ƙasar nan duba da irin halin da ‘yan ƙasa suka samu kan su s wannan lokaci.
Dakta Udon Emmanuel wanda ya ce da Katsina da kuma jihar Akwa Ibom ‘yan biyu ne da aka haifa rana ɗaya a ƙarƙashin shugabancin tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida saboda haka a cewar sa jihar Katsina da Najeriya na buƙatar mutum irin sa.
” Ina da kwarewa ta fannoni daban daban musamman ta fuskacin tattalin arziki da samar da ayyukan yi da kawo tsare tsare da za su ciyar da Ƙasa gaba, wannan tasa nake neman a bani dama domin fitar da Najeriya daga halin da take ciki” in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan har ya zamu nasarar zama shugaban ƙasa to jihar Katsina zata zama wata cibiyar kasuwanci, ya ce yana da dalilin faɗin haka saboda yana da manufa ta dawowa da martabar Katsina da ta rasa a wannan lokaci.
Haka kuma Gwamna Udon Emmanuel ya ce idan jihar Katsina yana son dawowar hulɗar tattalin arzikin jihar Katsina to ga hanya mafi sauki shi ne a zaɓe shi a ranar zaɓan fidda gwani da za a gudanar nan gaba kaɗan, wannan zai ba shi nasarar zama shugaban ƙasa a baban zaɓe mai zuwa
Ya ce idan har kana tunanin dawowar zaman lafiya da aka rasa da kuma yalwar abinci wanda yanzu ana fama da yunwa da talauci da kuncin rayuwa, to Udon Emmanuel shi ne amsar waɗannan tambayoyi.
“Zan tabbatar da tsaron jama’a jihar Katsina da dukiyoyin al’umma da suka haɗa da kasuwancin su dukkan mutanen Katsina za su samu amincin tsaro a ƙarƙashin gwamnatina idan na samu nasarar zama shugaban ƙasa” inji Udon Emmanuel
A cewar sa jihar Katsina ta samu ayyukan raya ƙara a ƙarƙashin mulkin tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema saboda haka tana buƙatar wani mutum zai ɗora irin wadancan ayyukan da aka rasa.
Tunda farko sai da shugaban riko na jam’iyyar PDP a jihar Katsina Alhaji Salisu Lawal Uli ya yi jawabin lalle marhabin da Udon Emmanuel da ‘yan tawagarsa kafin daga bisani ya gabatar masa da masu zaɓan fidda gwani (Delegates)
Gwamna Udon Emmanuel ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Benue Gebrial Suswan wanda kuma shi ne shugaban yakin neman zaɓansa a wannan tafiya.
