September 18, 2026

Idan An Inganta Noma A Inganta Kiwo!

0

Daga Mauzu Umar Hardawa

Allah ka ceci muhallin arewa da arzikin gandun daji da kiwo da rayukan masu dabbobi da ake tsiyatawa.

Tsadar man kananzir da iskar gas da ake girki sun sa ana ta sare daji don neman ice da gawayi.

An sare dazukan kusa da gari don abinci ko neman kudin sayen abinci.

Manyan dazukan da suka rage kuma ana ta mai da su gonaki, ana ta sare itatuwa da gandun dajin da dabbobi za su shekara suna kiwo da samar da dabbobi da zuma da magunguna da nono da man shanu yanzu sun koma hannun manoman da masu kudi.

Ya zamo wajibi hukumomi su lura da hatsarin cinye gandun daji babu farauta da labin shanu don a rage kashe makiya saboda filin neman noma.

A sani yawancin makiyaya basu iya noma ba basu iya kasuwanci ba, wasu babu karatun Allah babu na boko idan an cinye filayen kiwo an.sace dabbobi da suka mallaka dole su yi ta’addanci su nemi abinci ko da tsiya ko da arziki.

Saboda su da iyalansu kan kiwo suka dogara idan an ci gaba da tsiyata su akwai barazana.
Ya kamata idan an yi shelar inganta noma ayi ta inganta kiwo da gandun daji don arzikin makiyaya da zaman lafiyar Nigeria. Allah ya bamu zama lafiya.

Daga Muazu Hardawa Edita jaridar Alheri.
07011546797

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *