September 18, 2026

Hoto Ko Bidiyon Tsiraici: Wayar Hannu Bata Da Cikakken Aminci

0

Da yawa mutane suna da wannan ɗabi’ar ta “Denying Fact”, ƙiri da muzu an san da matsala sai ayi ya kauce kaucen cewa babu, wasu ma su dinga zagin wanda yace akwai matsalar.

Kamar haka ne akan wannan batu na wasu matasa da suke ɗaukar hoton tsiraicin su a waya, wasu suna yi ne su ajiye dan kawai suna so, wasu suna yi ne su aikewa masoyan su, wasu suna yi ne su aikawa abokan tarayyar su. Sai dai babban abinda ke ingiza su ga hakan shine yawan kallon finafinai na batsa wato ‘Pornography’.

Ba shakka ana samun wannan matsalar a tsakanin matasa da dama ciki har da waɗanda ake musu kallon wayayyu, kuma ba wai baƙon abu bane a yanzu, al’amari ne da ya zama ruwan dare tsakanin matasa maza da mata.

Shi yasa wasu da dama a wayoyinsu suke ɗauke da wasu manhajoji da mutum zai iya sanya kalmomin tsaro ya ɓoye ire iren waɗannan hotuna a wayar, sai sanda bukatar su da hotunan ko bidiyoyin ta taso su kalla. Manhajojin sun haɗa da wata Calculator dake bada damar ajiya, App Lock, Wani nau’in agogo da ke bada damar ajiya, Vault da makamantansu.

Hatsarin da ke cikin hakan bayan rashin dacewar sa abin yi, akwai matsalar fitar wannan abinda kuka boye zuwa wani (Third Party), kasancewar babu wani ingantaccen tsari a ƙasar nan da zai tsare abubuwan ka ga barin fita, ga kuma madatsa (Hackers) da kullum suke gwada ƙwarewar su ta hanyar datsar bayanan mutane.

Idan mutane basuyi taka tsantsan ba, za su cigaba da afkawa tarko saboda kokarin magance matsalolin su na shahawa, sawa’un saurayi da budurwa ne ko mata da miji, ya kamata su san cewa wayoyin hannu basu da cikakken aminci, idan ba za a ƙi yi don Allah ba, a nisanci hakan saboda gudun abinda ka je ya dawo. Wayar hannun ku bata da cikakken tsaro.

In kunne yaji……..
Allah ya shirye mu gaba daya albarkacin Annabi Muhammadu SAWA

Malam @Aliyu Samba

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *