September 16, 2026

Hon. Ɗanlami Ga Hon. Iro Isansi: Bani Da Alaƙa Da Matasan Da Aka Ce Sun Yi Maka Ihu.

0

Daga El-Zaharadeen Umar

Kwamishinan jin daɗi da walwala na jihar Katsina Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya nisanta kansa da wasu rahotanni ke yawo a kafar sadarwa ta zamani cewa ya tura wasu matasa sun kaiwa Dan majalisa farmaki.

Kwamishinan ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina, inda ya ce baya da wani dalili na tura kowane Irin mutum ya kaiwa wani farmaki saboda siyasa kuma a jami’yya ɗaya.

Wasu faya-fayen bidiyo da aka ga fusatatun matasa suna yawo a kafar sadarwa ta zamani inda wasu matasa suka yi wa ɗan majalissar tarayya Hon. iro Isansi Ihu da hayaniya, kuma aka danganta matasan da cewa yaran Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ne.

Ko shakka babu wannan abin ya tayar da kura so sai musamman a tsakanin gidajen guda biyu, inda kuma yatsan zargin ke nuna magoya bayan Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ne suka kai wancan farmaki, batun da Hon.Sani Aliyu ya ce baya da wata alaƙa ta nesa ko ta kusa da waɗancan matasan.

“Duk da cewa shi wanda aka yi wa abin bai kai ga fitowa fili ya yi magana ba, amma dai ya kamata mutanen Katsina ta tsakiya da ma jihar Katsina su sani cewa ni Hon. Sani Aliyu Ɗanlami bani da wani dalili na siyasa da zai sa in tura matasa su yi wani buyagi kuma a jami’yya ɗaya”inji shi

Haka kuma kwamishinan ya ƙara da cewa kwanan nan gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kafa wani kwamiti da zai yaki irin wannan ɗabi’a ta ‘yan bangar siyasa wanda kuma Hon. Sani Aliyu Ɗanlami yana goyan bayan haka, a cewarsa me zai sa ya yi wasa da wancan umarni da gwamna Masari ya bada.

Daga nan sai Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya bada tabbacin cewa duk wanda yake siyasa tare da shi ya zama wajibi ya mutunta saura jama’a, kuma bai yarda da cin mutuncin ko cin zarafin tare da sharri ko ƙage ga kowane ɗan siyasa ba.

Haka kuma ya bayyana cewa duk ke siyasar gidan Ɗanlami dole zai kasance mutum wanda yasan mutuncin jama’a ta yadda za a yi siyasa bisa bin doka da oda a Katsina ta tsakiya da ma jiha baki ɗaya

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *