Harin Kuje: Wadume Na Cikin Wanda Suka Gudu A Gidan Yarin.
Sannan ne mai garkuwa da mutanen nan kuma mai safarar makamai wanda ake cema Hamisu Wadume an bayyana cewa yana cikin wanda suka tsere a lokacin harin da ƴan ta’adda suka kai a gidan yarin Kuje.
Wadume dake tsare a gidan yarin Kuje bisa aikata laifukan fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma safarar makamai ba a sake jin duriyar shi ba.
Jaridar Daily Sun ta ce wanda ake zargin dake gidan yarin tun a shekarar 2020 na cikin bursunonin da jami’an tsaro suka sake kamowa.
Idan dai za a iya tunawa rundunar yan sandan Najeriya ce ta kama Wadume bisa zargin addabar jihar Taraba. Saidai jami’an tsaron yan sandan da suka kama shi na sashen IRT sun faɗa tarkon sojoji na bataliya ta 93 dake Takum a jihar Taraba, inda aka kashe jami’an yan sanda 3 daga cikinsu da kuma wani farar hula 1 a lokacin kamo shi.
An bayyana cewa sojojin da suka kubutar da Wadume sun yi haka ne karkashin umarnin kwamandan su mai suna Major Balarabe.
Kisan yan sandan dai ya haifar da Allawadai daga bangaren jama’a. Saidai daga bayan Allah ya ba yan sanda sa’ar sake kama Wadume a Kano, daga nan aka kai shi Abuja inda kuma aka miƙa shi kotu da ta kai shi ajiya gidan kaso.
