Harin Jirgin Kasan Edo: Yan Sanda Sun Kama Sarakunan gargajiya 2, Da Wasu 5.
A jiya ne gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa an kama wasu sarakunan gargajiya guda biyu da wasu mutane biyar da ake zargi da hannu wajen garkuwa da fasinjojin jirgin kasa 20 da aka yi a ranar Asabar, 7 ga watan Janairun 2023, wadanda ke dakon jirgi daga Igueben zuwa Warri a jihar Delta.
Kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar, Chris Nehikhare ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Benin.
Chris Nehikhare, wanda bai bayyana sunayen sarakunan biyu ba, ya ce an kubutar da mutane biyun da aka yi garkuwa da su na karshe daga hannun wadanda suka sace su.
Ya sanar da cewa yanzu haka mutane bakwan da aka kama ana bincikensu a hedikwatar ‘yan sandan jihar.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Godwin Obaseki ya zargi gwamnatin tarayya da rashin samar da ingantaccen tsaro a tashar jiragen kasa duk da abinda ya faru akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda aka yi garkuwa da fasinjoji da dama, tare da shafe watanni kafin masu garkuwa da su su sake su.
Gwamna Obaseki ya kuma zargi sarakunan gargajiya na yankin da rashin kula da lamarin, acewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.
