September 18, 2026

Har Gobe Jihar Katsina ta APC Ce –Gwamna Raɗɗa

IMG-20260305-WA0012

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya sake jaddada cewa Jihar Katsina na nan daram a matsayin jiha mai cikakken goyon bayan jam’iyyar APC bayan nasarar gudanar da zaɓen shugabannin a matakin mazaɓu ƙananan hukumomi da kuma jiha

 

 

Gwamna Raɗɗa ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar APC na jiha da aka gudanar a Katsina, wanda ya haɗa wakilai daga mazaɓu 361 da ke cikin ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina

 

A yayin taron, an zaɓi sabon Kwamitin Zartarwa na APC na Jihar Katsina ta hanyar sasanci, inda Hon. Bishir Gambo Saulawa ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar na jiha, tare da Alhaji Bala Abu Musawa a matsayin mataimakinsa.

Da yake jawabi, Gwamna Raɗɗa ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari, yana mai cewa hakan ya nuna haɗin kai da kuma ƙwarewar jam’iyyar APC a jihar.

 

Ya kuma taya sabbin shugabannin murna, yana mai cewa nasarar da suka samu wata dama ce ta ƙara hidima ga jam’iyya da al’ummar jihar.

 

Haka kuma ya yi alƙawarin cikakken goyon baya da haɗin kai daga gare shi a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar Katsina

Gwamnan ya kuma sake tabbatar da goyon bayan Jihar Katsina ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma manufofin gwamnatin tarayya.

 

Tun da farko, Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Tukur Ahmed Jikamshi, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne bisa ƙa’idojin dokar zaɓe da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.

 

A nasa jawabin, sabon Shugaban APC na jihar, Hon. Bishir Gambo, ya yi alƙawarin gudanar da ayyukansa da gaskiya da adalci tare da ƙarfafa haɗin kai a dukkan matakan jam’iyyar.

 

Daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka halarci taron akwai tsohon Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, Mataimakin Gwamna Faruk Lawal Jobe, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha Nasir Yahya Daura, da sauran manyan ‘yan siyasa na jihar.

About The Author