Hakimin Kaita Ya Rasu!
Allah ya yi wa Sarkin Sullubawan Katsina Hakimin Kaita, Alhaji Abdulkarim Kabir Usman rasuwa yanzun nan a asibiti gwamnatin tarayya da ke Katsina
Za a yi jana’iza da karfe 5:00pm na Yamma a kofar gidan Sarkin Katsina.
Muna rokon Allah ya jikansa da rahama ya kyautata na mu karshen idan ya zo.
