September 17, 2026

Gwamnatin Tarayya Ta Gano Ma’aikatan Bogi 1,000 A Ma’aikata Ɗaya.

0

Gwamnatin tarayya ta gano kimanin ma’aikatan gwamnati kimanin dubu daya, tare da tsaida albashin ma’aikata sama da 3,000 tsakanin shekarar 2012 zuwa 2020 saboda ma’aikatan sun ki zuwa a tantance su.

Gwamnatin tarayyar ta kuma ce, ta gano takardun daukar aiki na bogi guda 5,00 a wasu ma’aikatu, sassa, da hukumomi daban a yayin da take gudanar na wani shirin tantancewa na kasa.

Jaridar Leadership ta ce, Shugabar ma’aikata ta gwamnatin tarayya Dr. Folashade Yemi Esan ce ta bayyana hakan a lokacin gudanar da wani taron kasa da hukumar bankado masu yima tattalin arzukin Najeriya zagon kasa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *