September 18, 2026

Gwamnatin Raɗɗa Ya Ɗauki Ma’aikatan Lafiya 254 Domin Bunƙasa Harkar Kiwon Lafiya A Jihar Katsina 

FB_IMG_1730726458740

Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ta bayyana cewa zuwa yanzu ta ɗauki ma’aikatan lafiya guda 254 da nufin ƙara inganta ɓangaren kiwon lafiya a jihar baƙi ɗaya

Ma’aikatan lafiyar sun haɗa da Likitocin da Unguwar Zoma da masu aikin gwaje-gwaje da masu kula da harkokin magunguna sannan shirye-shirye sun yi nisa wajen ɗaukar ma’aikatan kashi na uku.

mataimakin gwamnan jihar Katsina Malam Faruƙ Lawal Jobe ne ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da aka saba shiryawa duk ƙarshen wata a Katsina

Malam Faruƙ Lawal Jobe ya ƙara da cewa gwamnati ta dauki matakin kawo ƙarshen matsalar likitoci da ake fama da ita inda yanzu haka mutum 41 sun ƙasar Masar domin koyan aikin likita da za su maye gurbin wancan matsala.

Mataimakin gwamnan ya cigaba da bayanin cewa an kashe kimanin naira 2,449,899,800.00 wajen ɗaukar nauyin karatun mutum 41 a ƙasar Masar.

Waɗannan kuɗaɗen a cewar sa, sun kunshi kuɗaɗan makaranta da na wurin kwana da na zirga-zirga da litattafai da kuma alawus-aliawus din su har zuwa lokacin da za su kammala karatun baƙi ɗaya

A cewar mataimakin gwamnan gwamantin jihar Katsina ta amince da sake duba tare da inganta albashi Likitocin gida domin magance karancin su da jihar ke fuskanta..

Haka kuma an ware kimanin naira miliyan 26,900,000:00 domin waɗannan likitoci su ƙaro karatun a manyan makarantun kiwon lafiya da ke cikin gida Nijeriya

“Duk a ƙoƙarin wannan gwamnati na bunƙasa harkar kiwon lafiya,ta kashe kimanin naira biliyan 13 domin ɗaukaka darajar ƙananan asibitoci guda 146 a faɗin jihar Katsina tare da da samar santoci huɗu a duk ƙananan hukumomi 34 da na jihar Katsina’ inji shi

Kazalika mataimakin gwamnan ya ƙara da gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta amince da da daukaka darajar wasu asibitoci da suka haɗa da na ƙananaa hukumomin Rimi da Faskari da Dandume da kuma Zango akan kuɗi ₦3,702,050,724.00

Sannan gwamnatin jihar Katsina ta kammala aikin daukaka darajar babbar asibitin Kafur wanda suka gada a tsohuwar gwamnati da kuma ta Kankia akan kuɗi ₦739,523,894:59

Sai kuma ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na maida cibiyar tsare masu lalurar Corana zuwa asibitin masu lalurar taɓin hankali akan kuɗi naira na gugar naira har naira miliyan ₦65,845,895:00

Daga ƙarshe ya bayyana cewa tsohuwar asibitin masu lalurar taɓin hankali za a ɗaukaka darajar ta sannan a haɗe ta da makarantar koyar aiki jinya ta Katsina Nursing and Midwifery wanda aka ware naira miliyan ₦478,395:00

About The Author