Gwamnatin Najeriya Ta Nemi Afuwar Dalibai da Iyayensu Kan Yajin Aikin ASUU.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nemi afuwar dalibai da iyayensu bisa yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi a wannan Juma’ar.
Da sanyin safiyar yau Juma’a ne shugabannin malaman jami’o’in gwamnati suka dakatar da yajin aikin na tsawon watanni takwas da suka fara a ranar 14 ga watan Fabrairu sakamakon gazawar gwamnati wajen shawo kan wasu matsalolinsu.
Gwamnatin tarayya ta bakin ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta nuna godiya ga daukacin ‘yan Najeriya da suka shiga taruka daban-daban a tattaunawar da ta kai ga janye yajin aikin.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai na Ma’aikatar, Olajide Oshundun, ya fitar, ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa da irin matakan da gwamnatin tarayya ke dauka, daliban Najeriya za su cike giɓin yajin aikin da aka yi.
A cewar sanarwar, “ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya mika godiyarsa ga kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila da shugabancin majalisar wakilan.
“Muna matukar farin ciki da kokarin Sarkin Musulmi, Alhaji Saad Abubakar III, da tsohon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Rev. Supo Ayokunle, da daukacin ‘yan kungiyar Kiristocin Najeriya da kuma Cocin Katolika ta Najeriya wanda hikimarsu ta taimaka aka gyara yajin aikin, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.
