September 17, 2026

Gwamnatin Katsina Ta Kwace Gonaki Da Dazuzukan Da Aka Raba Ba Bisa Ƙa’ida ba. 

0

Gwamnatin Katsina Ta Kwace Gonaki Da Dazuzukan Da Aka Raba Ba Bisa Ƙa’ida ba. 

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya amince da rahotan da kwamitin da aka kafa domin ya binciki yadda aka yi watandar filaye da gonaki ba bisa ƙa’ida ba,.

Haka kua a gwamnan ya sake kafa wani kwamitin da zai aiwatar da wannan aiki.

Bayanan haka na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren Gwamnatin jihar Katsina Abdullahi Aliyu Yar’adua ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai a Katsina

Sannan Kwamitin binciken ya bada Shawara cewa duk wanda ya san ya mallaki gone ko daji ta ɓarauniyar hanya ya yi wa kansa kiyamul Laili ya bar wajan kafin a iske shi.

Haka kuma kwamitin ya ce ya kamata jama’a su ƙara sani cewa gwamna ne kaɗan yake da ikon amincewa a bada fili a cikin birane, ba wani ba.

Kazalika kwamitin ya gargadi jama’a da su yi amfani da wannan bayani domin gujewa fadawa fushin hukuma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *