November 18, 2026

Gwamnatin Kano Ta Gayyaci Ganduje Kan Bidiyon Cin Hanci.

0

Yayin da Ganduje yake gwamna, an naɗi hoton bidiyonshi yana karbar daloli daga hannun wani dan kwangila tare da zubawa a cikin rigarshi.

Hukumar amsar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta ce ta gayyaci tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da ya gurfana a gabanta bisa zargin faifan bidiyo na cin hancin dala.

Yayin da Ganduje yake gwamna, an naɗi hoton bidiyonshi yana karbar daloli daga hannun wani dan kwangila tare da zubawa a cikin rigarshi.

Shugaban hukumar Muhuyi Rimingado ne ya tabbatar da sammacin ga manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Rimingado ya ce hukumar na sa ran Ganduje ya gurfana gaban ta a mako mai zuwa domin samun damar wanke kansa akan binciken da ake yi.

“Na sanya hannu a takardar gayyatarsa domin yi masa tambayoyi a hukumar a mako mai zuwa, saboda haka doka ta ce, kuma za mu ba shi dama ya kare kansa, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta Premium times ta bayyana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *