September 18, 2026

An Ceto Mutane 57 Da Ake Koƙarin Safararsu Daga Nijeriya Ta Hanyar Jihar Katsina.

0

An ceto mutanen ne akan hanyar Jibia da ke cikin jihar Katsina, wadda ke zama jihar Najeriya mai iyaka da jamhuriyyar Najar a jiya 04/07/2023.

Kwamandan hukumar yaki da safar bil’adama ta Najer Musa Aliyu ya tabbata da hakan ga manema labarai.

Kamar yadda ya bayyana, mutanen da suka ƙunshi maza da mata su 57, sun fito ne daga sassan Najeriya daban-daban.

Kuma suna ofishin hukumar, inda daga nan za a maida su ga iyalansu da zarar an kammala bincike.

Hukumar haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina ta bangaren sashenta mai yaƙi da safarar bil’adama da shan miyagun kwayoyi na yin wannan aiki na yaƙi da safarar bil’adama don ganin an magance matsalar.

Inda suka ce sun samu nasarori da dama.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *