September 19, 2026

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Haramta Barace-Barace A Kan Titinan

0

Dag wakilinmu

Gwamnatin jahar Kwara ta haramta barace barace a kan titinan dake Illorin babban birnin jahar.

Kwamishiniyar jihar akan bunƙasa rayuwar al’umma Aboseke Aremu ce ta sanar da hakan a lokacin taro da masu ruwa da tsaki a Ilorin.

Kamar yadda ta bayyana, gwamnatin jahar ta ɗauki wannan matakin ne duba da yadda barar ke zama abun damuwa a kan manyan yanyoyin dake cikin babban birnin jahar.

Kwamishiniyar ta kuma ce ma’aikatar da wakilan Hausawa sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna kan batun haramta barar.

Aboseke Aremu na kuma tuna ma mazauna jahar hukuncin da zai hau kan duk wanda ya karya dokar, wanda ya haɗa da cin tara ko kuma kaiwa gidan gyaran hali watau gidan kaso.

Wakilan Hausawan a jahar Surajadden Hussaini, da Rufa’i Sani, da kuma Muhammad Lawal sun ba jahar tabbacin goyan bayan su wurin hana barar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *