September 17, 2026

Gwamnatin Dikko Raɗɗa Ta Kasa Wajen Samar Da Bayanai Ga Al’ummar Jihar Katsina Cewar Dakta Mohammed B Tanimu

0

Gwamnatin Dikko Raɗɗa Ta Kasa Wajen Samar Da Bayanai Ga Al’ummar Jihar Katsina Cewar Dakta Mohammed B Tanimu

Ɗan kishin ƙasa kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar ‘Accord Party’ ya bayyana cewa salon da gwamnatin Dikko ta ɗauka na amfani da ‘yan social media wajen sanar da al’ummar halin da ake ciki ba zai wadatar ba.

Dakta Mohammed Tanimu ya bayyana haka a lokacin zantawa da manema labarai a Katsina

Ya ƙara da cewa yin amfani da kafafen yaɗa labarai na gaske zai taimaka wajen sanin me ke faruwa a wannan gwamnati ba tare da shakku kowa wasi-wasi ba.

Yana mai cewa yin amfani da kafafen sadarwa na zamani ba za su wadatar ba wajen sanin wane halin gwamantin take ciki.

“Yin amfani da kafafen yaɗa labarai da kowa ya amince da su zai taimakawa gwamnatin jihar Katsina kwarai da gaske wajen sanar da al’ummar irin ayyukan da take yi da kuma wadanda suka kan hanyar yin, amma social media ba za su iya wannan aiki ba” inji shi.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Malam Dikko Umar Raɗɗa da ta yi ƙoƙari wajen ganin an kammala wasu ayyuka da gwamnatin tarayya ta fara yi amma ba a ƙarasa ba, yana mai cewa Dikko Raɗɗa yana da fada a gwamantin Tinubu.

Dakta Mohammed Barau Tanimu ya nuna buƙatar da ake da ita, na bin ƙa’idoji kafin a bada kwangila a gwamanti, wanda ya ce babu bayanan yadda gwamnatin Dikko ke bada kwangila a sahihan kafafen yaɗa labarai

Kazalika ya bayyana cewa duk irin ƙarancin bayanan da gwamnatin take da su ga al’ummar jihar Katsina haka ba zai hana su ganin wasu ayyukan alheri da gwamnatin ta yi ba, sai dai ya ce rashin bayani ke sa mutum ba zai ce komi ba.:

Dakta Mohammed ya ce ya yi imanin cewa gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa zai saurari ire-iren waɗannan shawarwari domin ciyar da gwamnatin sa gaba ta fuskar samar da bayanai ga al’ummar jihar Katsina

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *