Gwamnan jihar Katsina ya Kaddamar da rijoyi guda Dari Biyu Da ashirin (220) Tare da injinan Ban ruwa ga manoman Rani Na Shiyyar Funtua.
Daga Abubakar Shafi’i Alolo Mobile Media Crew
A ranar Lahadi 26/12/2021, Gwamna jihar Katsina. Rt. Hon. Aminu Bello Masari CFR, ya kaddamar da aikin alherin da Sanata mai wakiltar shiyyar Funtua Sanata Bello Mandiya ya assasa, Domin cigaban Al’ummar yankinsa a garin Nahuta iyakar Katsina da Kaduna dake cikin karamar hukumar Danja, cikin Shiyyar Funtua.
Kowace Karamar hukuma dake Shiyyar Funtua cikin guda goma Sha daya ta amfana da injinan ban ruwa guda 20, tare da gina rijiyoyi a fadamunsu domin su cigaba da noman rani, hakan zai kara bunkasa harkar noman Rani duba da yanda ake fama da tsadar rayuwa.
Da yake Jawabin maraba yayin gudanar da taron shugaban Jam’iyyar Apc na karamar hukumar Danja. Hon. Isa Ali Dan Maigauta, Ya yi” godiya ga Allah SWT, wanda da ikonsa ne yasa aka gudanar da wannan aikin alheri da sanatan ya assasa, wanda hakan zai samar da abun yi ga dimbin matasa dake shiyyar ta Funtua.
Shima a nashi jawabin mataimakin shugaban Jam’iyyar Apc mai kula da Shiyyar Funtua Hon. Ibrahim Danjuma ya yima Allah SWT godiya daya basu Sanata Bello Mandiya a matsayin Sanata a shiyyar Funtua.
Da yake jawabin godiya amadadin al’ummar yankin fadamar Garin Nahuta da su ka amfana da tallafin, Tsohon kantoman riko na karamar hukumar kankara Hon.
Anas Isah Kankara, ya bayyana Sanata Bello Mandiya a matsayin jajirtacce wakili wanda ya kamata ace ana koyi da shi.
Shima a nashi jawabin Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Wanda ya samu wakilcin Alh. Ibrahim Tukur Jikamshi Shugaban hukumar saka hannu jari ta Jihar Katsina ya yaba da kokarin Sanata Bello Mandiya akan yadda ya dauki harkar noma da mahinmanci. Duba da noma na daya daga cikin kudurorin shugaban kasa Muhammad Buhari. Daga karshe yaja hankalin wadanda su ka amfana da tallafin Injinan da suyi amfani dasu yadda ya dace.
Bikin ya samu halartar Gwamna jihar katsina wanda ya samu wakilcin Shugaban hukumar saka hannun jari Alh Ibrahim Tukur Jikamshi, mataimaki na Musanman ga sanatan Hon. Abdul’aziz Lawal Dan Yari, Alh Maigoro hukuma Malumashi, Alh Sagir Karfi, Alh Ibrahim Mai Bulo Funtua, Alh Audu Liti.
Sauran sun hada da Hon. Hussaini Hashim Dabai, Alh Salisu Garewa Sabuwa, Hajiya Saratu Danja Shugabar mata ta Jama’iyyar Apc ta Shiyyar Funtua, Mataimaki na Musamman ga Sanatan Hon. Aminu Ibrahim Kafur, S.A Mansur O.O
