September 17, 2026

Gwamna Raɗɗa Zai Sanya Fitilu Masu Amfani Da Rana 10,830 A Makarantun Tsangaya a Katsina 

FB_IMG_1781771331027

Gwamnatin jihar Katsina Ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta amince da sanya fitilu masu amfani da hasken rana a makarantun tsagaya guda 361 da ke fadin jihar.

 

Wannan mataki ya biyo bayan zaman majalisar zartarwa ta jihar Katsina da ya gudana a fadar gwamnatin jihar.

 

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa, mai baiwa gwamna shawara akan harkokin wutar lantarki da makamashi, Dakta Hafiz Ibrahim ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa ga makarantun tsagaya

 

A cewar sa, ɗaukar wannan mataki zai taimaka matuƙa gaya wajen samar da tsaro a makarantu wanda yana cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina na zamantar da da tsari ilimin almajirai da haɗa cikin tsarin ilimin zamani.

 

Ya ƙara da cewa kowace mazaɓa za a sanya waɗannan fitilu guda 30 domin samar da haske da zai taimaka wajen kawo tsaro a wuraren da aka sanya waɗannan fitilu.

 

Dakta Hafiz Ibrahim ya yi bayanin cewa majalisar zartarwa ta amince da aiwatar da tsarin nuna alama ga kasafin sauyin yanayi a dukkan ma’aikatun gwamnatin jihar Katsina.

 

Ya ƙara da cewa tsarin zai shafi ƙananan hukumomi da hukumomin gwamnati wanda ya ce tsarin zai shafi dukkan wasu shirye-shirye da ayyuka da suke da alaƙa da kashe kuɗaɗen gwamnati da suka danganci sauyin yanayi.

 

“Wannan tsari zai taimaka wajen ƙara ƙaimi da tunkarar sauyin yanayi tare da inganta gaskiya da rikon amana da kuma inganta tafiyar da kuɗaɗen gwamnatin jihar Katsina” inji shi

 

Ya ƙara da cewa, “wannan shiri zai ƙara ƙarfin juriya ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki, inganta noman abinci, ƙarfafa kula da albarkatun ruwa, da kuma tallafawa ci gaba mai ɗorewa a fannoni masu muhimmanci.”

 

Haka kuma, Hafiz ya tuna cewa gwamna Raɗɗa ya kafa tarihi a baya-bayan nan a taron “Change NOW 2026” da aka gudanar a birnin Paris na ƙasar Faransa, inda ya zama ɗaya daga cikin shugabanni daga Nijeriya na farko da ya gabatar da muhimmin jawabi a taron na duniya.

 

A yayin taron, gwamna Raɗɗa ya bayyana sauye-sauyen da jihar ke yi a fannin makamashi mai sabuntawa, ciki har da shirin farfaɗo da kamfani mai amfani da Iska da ke lambar Rimi (Wind Farm).

 

Ya ƙara da cewa wannan sabon amincewa daga majalisa na nuna ƙudirin gwamnati na mayar da manufofin da ake tattaunawa a tarukan ƙasa da ƙasa zuwa ayyukan ci gaba na zahiri a cikin gida.

About The Author