November 18, 2026

Gwamna Raɗɗa Zai Samar Da Tashar Wuta Mai Ƙarfin MEGA Watt 1 Daga Hasken Rana A Gidan Gwamnatin Jihar Katsina 

0

Aikin Samar Tashar Wutar Lantarki Mai Ƙarfin MEGA Watt Guda Daga Hasken Rana A Gidan Gwamnatin Jihar Katsina Ya Kankama

Aikin samar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana da za ta samar da wuta mai karfin MEGA Watt Guda a faɗar gwamantin Jihar Katsina zai canja tsari da yanayin jihar baƙi ɗaya.

Shugaban hukumar samar da wuta a ƙarkara da birane Alhaji Abubakar Matazu ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina, a lokacin da ya ke duba aikin.

A cewar shugaban hukumar, aiki na gwaji ne da jihar Katsina ta shriya domin rage kashe makudan kudade wajen biyan kamfanin taraba wuta na KEDCO da sayen Man gas don tayar da janareto.

Ya ƙara da cewa dalilin da yasa gwamantin Jihar Katsina ta yi tunanin yin wannan aiki shi ne, domin ta rage yadda take kashe miliyoyin naira wajen biyan kudin wuta, wanda ya ce ko a watan da ya gabata gwamanti ta biya miliyan 200 a gidan gwamanti kawai.

Alhaji Abubakar Matazu ya ƙara da cewa mahimmancin sanya samar da wannan tasha da zata samar da wuta mai karfin MEGA Watt Guda a gidan gwamnati da wasu asibitoci a jihar Katsina domin ya rage matsalar rashin wuta ake fama da ita da kuma irin ƙuɗaɗan da ake kashewa wajen sayen man gas da kudin wuta.

“Idan aka kammala wannan aiki zai baiwa gidan gwamnati wuta baki ɗaya, sannan an yi tsarin mai kyau ta yadda babu yadda za a samu matsalar ɗaukewar wuta awa 24.” Inji shi

Kazalika ya bayyana cewa dalilin faɗada wannan aiki zuwa wasu asibitoci shi ne, yadda narasa lafiya ke shiga wani hali saboda rashin wuta da cizon sauro wanda ka iya haddasa wata cuta, gashi kuma jihar Katsina tana da yanayin zafi so sai.

Shugaban hukumar samar da hasken wuta a ƙarkara da birane, ya ƙara da cewa yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa wajen fara aikin samar da wuta mai amfani da hasken rana mai karfin kilo wata 300 a babbar asibitin Katsina domin kyautata yanayin asibitin da kuma marasa lafiya.

Haka kuma Abubakar Matazu ya ce hatta fitilun manyan tituna na Katsina an bada aikin maida su zuwa haske rana wanda ya ce haka na iya jan ra’ayin masu zuwa hannu jari daga wasu ƙasashe.

Shima da yake ƙarin haske akan yadda aikin zai kasance injiniya Abdullahi Bature wanda shi ke kula da aiki sanya kayayyakin samar da wutar ya bayyana cewa aiki ne da zai taimaka matuƙa gaya wajen rage ɗumamar yanayi da duniya ke fuskanta.

Ya bayyana cewa za su kammala wannan gagarumin aiki da zai lakume kusan naira biliyan 2 a cikin watanni uku zuwa huɗu, ya ce kuma aiki ne na gwaji wanda ake sa ran za a ɓullo da wasu ayyukan nan gaba.

Yana mai cewa duk kayan da ake bukata domin kammaluwar aikin sun riga sun iso, abinda ya rage shi ne, aiki kuma tuni an fara, saboda haka suna fatan al’ummar jihar Katsina za su ga canji a wannan ɓangaren nan ba da jimawa ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *