September 18, 2026

Yadda Kasurgumin Ɗan Bindiga Ya Ƙaƙabawa Wasu Kauyuka Harajin 100,000 A Katsina

0
  1. Yadda Kasurgumin Ɗan Bindiga Ya Ƙaƙabawa Wasu Kauyuka Harajin 100,000 A Katsina

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina na cewa kasurgumin dan ta’adan nan Buzare ya ƙaƙabawa wasu al’ummomi harajin naira dubu dari ga duk mutumin da zai aurer da ‘yarsa mace.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da ‘yan bindiga suke tsare da mutumen garin Maidabino, mutum 83 da yawansu mata ne da ƙananan yara, yau kimanin mako uku ke nan suna hannun su.

Buzare dai ya yi wani taro a ranar lahadin da ta gabata a kauyen Leletu inda ya tara mutanen garin ya shaida masu wannan sabon haraji ko kuma su fuskanta farmaki.

Wata majiya daga garin Maidabino ta bayyanawa wakilinmu cewa duk budurwar da za a yi wa aure sai mahaifinta ya biya dubu ɗari lakadan.

Majiyar ta cigaba da cewa idan magidanci yana da ‘ya mace in dai a garin Maidabino take aure dole sai an biya waɗannan kuɗaɗai kafin a zauna lafiya.

Haka kuma babu wani jami’in tsaro da ya kai ɗauki wannan gari na Leletu da Maidabino domin kwatar mutane daga sharrin Buzare.

Mutanen Maidabino na cigaba da kokawa akan yadda gwamnatin jihar Katsina ta yi shakulatun ɓangaro da batun mutane 83 mafiyawan su mata da ƙananan yara da suke hannun ‘yan bindiga musamman rashin jajanta masu da kuma ɗaukar mataki.

Wasu bayanan sirri sun tabbatar da cewa da yawan jama’ar da ake yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa a wannan wuri na kauyen Leletu ake ajiye su.

An kuma bayyana Leletu a matsayin wuri mafi haɗarin wanda hatta jami’an tsaro ba sa iya zuwa wajen balanta su kai ɗauki ko ceton al’umma.

Yanzu haka dai gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya cilla hutun wata guda inda ya miƙa tafiyar da harkokin gwamnatin a hannun mataimakin sa duk da irin ƙalubalen tsaro da jihar ke fama da shi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *