September 15, 2026

Gwamna Raɗɗa Ya Gabatar Da Naira Biliyan N828,638 A Matsayin Kasafin Kudin Shekarar 2027

IMG-20260908-WA0019

 

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gabatar da kasafin kuɗin ƙarshe a wa’adin mulkin da na farko kimanin Naira Biliyan N828,638 a gaban zauren majalisar dokokin jihar Katsina domin amincewa da shi

 

Taken kasafin kuɗin wannan shekara dai shi ne ‘Gina Gobanka Kashi Na 4’ wanda kuma ya bada tabbacin cewa bisa buƙatun al’umma ne aka shirya kasafin kudin baƙi ɗayan sa.

Da yake jawabi a gaban zauren majalisar dokokin jihar Katsina gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa wannan kasafin kudin zai maida hankali ne wajen samar da ingantaccen ilimi da kiwon lafiya da ruwan sha da noma da harkar tsaro da sauran abubuwan more rayuwa.

 

Ilmi

 

A cewar gwamnan an ƙara yawan makarantun sakandare tare da ɗaukar sabbin malaman makarantu waɗanda za su da ce da yanayin koyo da koyarwa a dukkanin makarantu sakandire da ake da su a faɗin jihar Katsina.

 

Gwamna Raɗɗa wanda ya ce gwamnatin sa ta kashe kimanin Naira Biliyan 3.55 wajen ganiwa tare da kula da makarantu na musamman guda uku wanda tuna an fara harkokin karatu cikin ɗaya ta garin Raxixa

Ya ƙara da cewa an kashe Naira Biliyan 2.07 wajen kuɗin jarabawar ɗalibai ta SSCE da ta haɗa da WAEC da NECO da NABTEB da kuma NBAIS tare da haɗin gwiwa da ƙananan hukumomi 34 sannan ya ƙara da cewa kimanin Naira Miliyan 1.26 an kashe su wajen bada tallafin karatu ga ɗalibai na cikin gida da kuma na ƙasashen waje.

 

Gwamna Dikko Umar Raxxa ya qara da cewa a wannan shekarar ta 2026 gwamnatin sa ta bada tallata mata daban-daban a qananan hukumomi 34 tare da bada tallafin sana’o’i ga matasa domin su dogara da kan su.

 

Dangane da batun tsaro kuwa gwamnan ya bayyana cewa an samu sauki so sai inda ya ce manoma sun koma gonakin su a wannan shekara domin yin noma wanda hakan ke nuna irin nasarorin da aka samu.

Kiwon Lafiya

 

A ɓangaren kiwon lafiya ya ce babu wata mazaɓa cikin 361 da ake da su a faɗin jihar Katsina da babu wata cibiyar kiwon lafiya da bata aiki a kowane lokaci

 

Akan batun kiwon lafiya kuwa, gwamnan ya ce tsakanin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da manyan asibitoci guda 1,751 sun kai kashi 85 na ɗaukaka darajar su

 

Kazalika ya ƙara da cewa an kashe kuɗi Naira Biliyan 4.71 wajen samar da ayyukan kiwon na gaggawa tare da sayo motocin ɗaukar marasa lafiya tare da zuba jari a wasu asibitoci da magunguna da gine-gine

 

Malam Dikko Raɗɗa ya ce ɓangaren ruwan sha kuwa gwamnatin sa tana cikin wani ƙoƙari wanda yake aikin jawo ruwan Zobe Dam da zai ratsa ƙananan hukumomi 8 da za su amfana da ruwan sha mai tsafta dukkanin su.

 

Haka kuma gwamna Raɗɗa ya nuna buƙatar da ake da ita, wajen cigaba da samar da tsabtataccen ruwan sha inda ya bayyana cewa rijiyoyin burtsatse na nan a matsayin hanyar samar da ruwan sha ga mafiyawan magidanta

 

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa zata cigaba da tabbatar da zuba jari a ɓangaren ruwan sha tare da ƙoƙarin kai ruwa wurare daban-daban a ƙarƙashin shirin samar da ruwan sha na “Zobe Phase 1B Water Project’

About The Author