Gwamna Dauda Ya jinjinawa Sanata Yari Akan Ayyukan Da Ya keyi A Zamfara
Daga Hussaini Yero
Gwamnan Jihar Zamfara,Dr Dauda Lawal ya jinjinawa tsohon gwamna,Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar akan ayyukan da ya keyi na cigaban al’umma a yankin Talatar Mafara.
Gwamna Dauda yayi jinjinar ne a ziyar da ya kai a Ofishin Girandi Kadi da ke cikin Ma’aikatar shari’a da ke Gusau.
A jwabin sa gwamna Dauda ya bayyana cewa,ya samu labarin cewa, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar ya gyara koton Talatar Mafara,da kuma wasu ayyuka da yanzu haka ya keyi dan cigaban alumma.
Akan haka ne gwamna Dauda ya yabawa tsahon gwamna kuma yayi kira ga al’umar jihar da suyi koyi da Sanata Abdul’aziz Yari wajan ayyukan cigaban al’umma.inji gwamna Dauda”.
Gwamna Dauda ya tabbatar da cewa, shi kam a shirye ya ke ya amsa gayyatar tsahon gwamna Abudulaziz Yari,wajan bikin bude ayyukan da yayi dan cigaban alumm.
Kuma bamashi ba duk wani dan zanfara da yake sanyin ayyukan cigaban alumma muna maraba da shi.san yanzu ba lokacin siyasa bane lokaci ceton alumma ne da kowa ya kamata ya bada tasa Gudunmuwar.inji Gwamna Dauda Lawal.
