September 18, 2026

Gwajo-gwajo Ya Yabawa gwamnatin Jihar Katsina akan Bada Tallafin Abinci A watan Ramadan.

0

 

Gwajo-gwajo Ya Yabawa gwamnatin Jihar Katsina akan Bada Tallafin Abinci A watan Ramadan

Mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara akan harkokin siyasa Hon. Ya’u Umar Gwajo-gwajo ya yabawa gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Malam Dikko Umar Raɗɗa akan bada tallafin abinci ga mabuƙata da ta yi a cikin watan Ramadan.

Wannan yana kunshe ne acikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Katsina

Hon. Gwajo-gwajo Ya bayyana wannan gudunmawa a matsayin wanda aka yi ta daidai lokacin da ake buƙatar ta musamman yanayin da aka shiga da kuncin rayuwa a tsakanin al’umma.

Haka kuma ya ce abincin da aka rabawa al’umma zai taimaka wajen karewar farashin kayan abinci tare samar da yawan shi a cikin kasuwanni wanda zai yi sauƙin samu ga masara karfi

Tsohon Kakakin Majalisar ya ƙara da cewa wannan rabon tallafin abincin ya ƙara fitowa da tausayin gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ga jama’ar jihar Katsina wanda hakan na cikin alƙawaran da ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓe.

Mai baiwa gwamnan shawara ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su yi amfani da wannan sallah wajan yi wa Gwamna Raɗɗa addu’ar samun nasarar cika alkawarin da ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓe.

Daga ƙarshe ya roki al’umma da su cigaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya daga matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar Katsina da arewacin Nijeriya baki daya.

 

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *