September 18, 2026

Fiye Da Mutane 150 Ke Hannun ‘Yan Bindiga A Ƙaramar Hukumar Jibiya -Hon. Bishir Maitan

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Shugaban ƙaramar hukumar Jibia a jihar Katsina Hon. Bishir Sabiu Maitan ya bayyana cewa yanzu haka akwai fiye da mutane 150 da ke riƙe a hannun masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a ƙaramar hukumar Jibia.

Hon. Maitan ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake yi wa wakilan kafafen yaɗa labarai bayani irin kokarin da gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari akan ‘yan gudun hijira da ke makarantar ‘yan mata da GGSS Jibiya.

Shugaban ya ƙara da cewa kullum sai an kai hari a ƙaramar hukumar Jibia kuma kullum sai an ɗauki mutane da niyyar abiya kuɗin fansa kafin a samu su.

”Wannan al’amarin ya wuce duk ake tunanin sa, kusan yanzu na koma bani da wani aiki da wuce kula da ‘yan gudun hijira da kuma karɓar rahotanni na kai hare-haren wuce gona da iri daga ‘yan bindiga, kullum maganar ke nan.”in ji shi.

Ya ce da cewa yanzu haka akwai mutane 60 dukkansu ‘yan gari ɗaya suna hannun ‘yan bindiga ana ta ƙoƙarin ganin yadda za a kuɓutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane sai an bada kuɗin fansa.

A cewar sa jami’an tsaro da kuma ita kanta gwamnati suna koƙari so sai wajan ganin an kawo karshen wannan al’amari, amma fa an toshe can, sai can ya buɗe, Allah ya Kawo mana zaman lafiya inji shi.

Shugaban ƙaramar hukumar dai ya ce wannan adadin da ya ambata an ɗauke mutanen ne a cikin wata guda kacal, sannan ya ƙara da cewa a haka ma an sako wasu da iyalansu suka biya kuɗin fansa.

Ƙaramar Hukumar Jibiya dai tana cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga suka hana sakat, inda yanzu haka fiye da mutane dubu ashirin na gudun hijira wasu an Najeriya wasu kuma a jamhuriyar Nijar.

Haka kuma aikin ‘yan bindigar ya tilastawa da yawa daga cikin magidanta tserewa su bar iyalan su, wasu kuma tuni sun riga mu gidan gaskiya, amma babar matsalar ita ce yadda wannan al’amari yaki ci yaki cinyewa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *