September 18, 2026

Mutane 15 Sun Mutu An Haifi 35 Fiye Da Yara 3,000 Ba Su Zuwa Makaranta A Sansanin ‘yan Gudun Hijira Na Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Kiminin mutane 15 ne suka rasu kuma mafiyacin su mata ne, haka kuma an samu haihuwa aƙalla 15 a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina a cikin watanni uku da suka gabata.

Shugaban ‘yan gudun hijira Malam Sa’adu Salisu ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da tawagar ‘yan jaridu masu aikawa da rahotanni daga jihar Katsina suka kai ziyarar gani da ido a sansanin da ke makarantar ‘yan mata ta jibiya

Ya ƙara da cewa sun kai kimanin su dubu 16 da suka fito daga ɓangarori daban-daban da suka haɗa da Tsabu, Farfaru, Kwari da Garin Alhaji da Zango da Shinfida da sauran garuruwa da ke kusa da garin Jibiya.

Waɗannan mutane dai sun rasa muhalansu ne sakamakon haren -haren ‘yan bindiga da masu satar jama’a domin neman kuɗin fansa kuma labarin yaki ci yaƙi cinyewa.

Shugaban ‘yan gudun hijira ya ce wasu daga cikin yan gudun hijira basa kwana a sansanin sakamakon rashin wurin kwana mai kyau da rashin gidan sauro da lantarki da ruwan sha da sauran kayayyakin more rayuwa.

“Sannan muna fuskantar matsalar tsaro a wannan wuri, duk wannan yawan na mu ɗan sanda biyu ne kawai ke tare da mu, sannan yanayin da muke ciki abin ba daɗi jin musamman matsalar rashin abinci wadatacce.” In ji shi.

Haka kuma Malam Sa’adu Salisu ya ƙara da cewa lokacin baya suna samun abinci har sau uku a rana amma a hankali a hankali yanzu wani lokaci sau ɗaya suke cin abinci , ya ce wasu mutanen ma a ƙasa suke kwana saboda rashin isassun abin shinfida wasu kuma suna shinfida zannuwansu suna kwantawa.

Game da matsalar rashin lafiya kuwa shugaban ‘yan gudun hijira ya ce suna samun gudunmawar magunguna daga gwamnati da kungiyoyi da ‘yan siyasa da masu hannu da shuni

A cewar sa yanzu baban abinda ya fi damunsu shi ne yadda yaransu musamman mata ƙanana fiye da dubu uku ba sa zuwa makaranta saboda halin da suka tsinci kansu a cikin, ya ce lallai wannan matsala da ita suke kwana da ita suke tashi.

A ta bakin shugaban ƙaramar hukumar Jibia Hon. Bishir Sabiu Maitan ya ce duk abinda ‘yan gudun hijira ke bukata bakin gwargwado gwamnatin jihar Katsina na yi ba tare da wata matsala ba.

Hon. Maitan ya ce kullum sai an dafa buhun shinkafa goma sha biyar, kuma ya ce bashi da labarin cewa sau ɗaya ake abinci a sansanin ‘yan gudun hijira, domin gwamnati sau uku take bada abinci.

Ya ƙara da cewa babu wata buƙata da suka kaiwa gwamna Masari da bai yi masu ba, saboda haka gwamnati na bakin kokarin ta wajan kyautatawa ‘yan gudun hijira, sai dai ajizanci na ɗan adam ba za a rasa ‘yan kurakurai ba

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *