Fitinar Shari’ar PDP Ce Ta Hanani Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi Tsawon Shekaru Shida –Masari
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya dora alhakin rashin gudanar da zaban Kananan hukumomi tsawon shekaru shida akan babar jam’iyyar adawa ta PDP da ke bibiyarsa da batun shari’ar rushe shuwagabanin Kananan hukumomi a karkashin Jam’iyyar.
Masari ya bayyana haka ne a lokacin wata ganawa ta musamman da kafefan yada labarai a wani yanayi na maida martini game da zarge-zargen da jam’iyyar PDP a jihar Katsina ta yi masa na kin shirya zabe tare da kin bin umarnin kotun kolin da ta ce ya biya rusasun shuwagabanin KanananHukumomi da ya yi ba bisa ka’ida ba.
Gwaman Masari wanda ya ce matsalar kin yi zabe ta samo asali ne tun daga ranar da jam’iyyar PDP ta dauki matakin shari’a a kansa da gwamnatinsa kuma take kawo masa tarnaki wajan sha’anin gudanar da mulki a tsawon shekaru shida
“Sun kaimu kara baban kotun jiha, da baban kotun tarayya, da kotun daukaka kara har zuwa kotun koli ba sau daya ba, ba sau biyu, wanda hakan ya taimaka wajan hana mu samun sukunin da zamu gudanar da zabe a cikin lokaci” inji Masari
To sai dai a cewar gwamna Masari zance yanzu ba haka yake ba, domin kuwa a wannan shekarar an samu hukuncin kotun koli wanda tace a biya hakkokin korarun shuwagabanin Kananan Hukumomi da kansilolinsu duk wani hakkin na su.
Ya ce koda ba a rushe su ba, da yanzu sun kamala wa’adin mulkinsu sun kara gaba, ya kuma kara da cewa bayan jam’iyyar PDP ta dabaibaye batun zaban da shari’a sun koma daga gefe suna zargin cewa ba za a kulla mai kyua ba a zaban da za a gudanar a farkon shekara mai kamawa ta 2022
“Bayan hukuncin kotun koli mun kafa kwamiti mai karfin gaske wanda yanzu haka ya cimma kashi 98 wajan biyan hakkukin rusasun shuwagabanin Kananan Hukumomin da wannan kora ta shafa, sannan kuma mun kara kafa wani kwamitin da zai gudanar da zabe a farkon shekara mai kamawa ta 2022” inji shi
