September 17, 2026

Fashewar Wani Abu Ta Kashe Mutane 4 A Kogi A Daidai Lokacin Zuwan Buhari Jihar.

0

Wani abu ya fashe a garin Okene hedkwatar mazabar Kogi ta tsakiya, mahaifar Gwamna Yahaya Bello.

Fashewar ta faru ne sa’o’i kadan kafin ziyarar tarihi da ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar ta Kogi a yau.

Sai dai takaddama ta biyo bayan fashewar inda wasu ke danganta lamarin da tashin bam, wasu kuma na cewa taranfoma ce.

Sai dai rahotanni sun ce mutane uku ne suka mutu sakamakon fashewar abun data afku mitoci kadan daga fadar Ohinoyi dake titin Kuroko a Okene.

Tun jiya ne dai gwamnan yaje Okene yana jiran ziyarar farko da shugaban zai kai jihar tun bayan da ya karbi ragamar mulki a ranar 27 ga watan Janairun 2016.

Ana sa ran shugaba Buhari zai fara sauka Okene inda aka shirya gudanar da wani zama, da kuma buɗe wasu ayyuka a mazabar yankin, kafin ya wuce zuwa Lokoja, babban birnin jihar domin ci gaba da buɗe sauran wasu manyan ayyukan, inji jaridar Vanguard majiyar Popular News Hausa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *