An Sako Basaraken Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
Makusantan Mai garin Ummadau da ke ƙaramar hukumar Safana da aka ɗauka tare da mutane uku, sun tabbatar da ‘yan bindiga sun sako mai garin da yammacin yau Alhamis
An ɗauke mai garin n Alhaji Bara’u Zakka akan hanyar sa ta zuwa gangamin yakin neman zaɓen Ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC.
Wata majiya ta tabbatar ma da jaridun Katsina city news cewa wani kwamandan ‘yan bindigar mai suna Usman, akayi ma magana shi kuma yayi ma dabar da suka sace maigarin magana suka sako shi.
