September 18, 2026

Fagen Kimiyya: Me ke riƙe da Duniya? (III)

images - 2025-05-18T065029.591

Fagen Kimiyya: Me ke riƙe da Duniya? (III)

Tare Da Abubakar Isah Hassan

Sararin samaniya yana tamkar wani fili ne da ba shi da bango, ba shi da bene, kuma ba shi da ƙofa, a cikin duhun da bashi da iyaka. Amma cikin wannan fili akwai abubuwa masu ban mamaki da ke cike da hikima.

Duniya da muke zaune a kanta tana shawagi ne a cikin wannan fili kamar yadda zinariya ke shawagi cikin ruwa mai tsafta, ba tare da wani abu da ke riƙe da ita ba, ko goya mata baya a bayyane.

Wannan dalilin yasa zamu iya bijiro da wata tambaya domin nazari: me ke riƙe da wannan ƙwallon duniya a inda take? Kuma me ke hana ta faɗowa ko fita daga tafarkin da take bi? Mu leƙa mu gani:

Ka ɗan yi tunani kaɗan. Misali, ɗauki dunƙulen ƙasa ko dutsi ka riƙe a hannun ka, sai ka ɗauka kamar kana kallon wani dunƙulen dutsi dake a sararin samaniya, sai ka sake shi daga hannunka, Idan a duniya ne, ƙasa za ta janyo shi, ya faɗo. Amma a wajen ikon duniya, ƙwallon ba za ta faɗo ƙasa ba, sai dai ta ci gaba da shawagi a sarari.

Wannan yana nuna cewa akwai wani ƙarfi mai iko wanda ba ba’a gani da ido, wanda ke jan komai mai nauyi zuwa inda wani nauyi ya fi shi, shie ake kira da wato “gravity”.

Wani masanin kimiyya da ya rayu a ƙarni na 17, Sir Isaac Newton, shi ne ya fara gano wannan ka’ida ko ƙarfi bayan ya ga yadda tuffa ke faɗowa daga sama. Wannan al’amari da ya faru cikin sauƙi ya motsa tunaninsa, sai ya tambayi kansa: me ya sa tuffa ya faɗo ƙasa a madadim yayi sama?

Wannan tambayar ce ta haifar masa da fahimtar cewa lalle akwai wani ƙarfin da ke janyo duk wani abu mai nauyi zuwa ƙasa. Wannan shi ne dalilin da yasa komai ke faɗowa idan ba a tallafe shi ba. Amma fa, ba duniya kaɗai ce ke da wannan iko ko ƙarfin Maganaɗinsun ba.

Yadda abin yake shine: Rana tana janyo Duniya, Duniya tana jan Wata, wata kuma yana jan Ruwan teku da Koguna, wanda hakan ke haifar da tafiyar ruwa, wato tide.

Sai kuma wani shahararren masani, Albert Einstein, wanda ya fitar da sabuwar fahimtar da ta zarce ta Newton. A cikin iliminsa na General Relativity, ya bayyana cewa abubuwa masu nauyi suna karkatar da fili da lokaci. Wannan fili da lokaci, wanda ake kira space-time, yana iya lanƙwasawa kamar yadda tabarma ke lanƙwasawa idan a ka ɗora kwalba mai nauyi a kanta.

Wannan lanƙwasa yana sa sauran abubuwa su shiga tafarkin zagayawa, ba wai domin an janyo su da igiya ba, sai domin suna bin wannan lanƙwasar da nauyin ya haifar.

Idan ka yi tafiya a gab da rami, ko da ba ka gan shi sosai ba, zaka iya karkata cikin sa. Wannan shi ne irin yadda gravity ke aiki. Rana saboda nauyinta mai girma, tana lanƙwasar sarari da lokaci a kusa da ita.

Wannan yasa duniya ke zagaya rana a tafarki mai kyau, ba tare da fadowa ba. Wannan tsari yana da ban al’ajabi, domin yana ci gaba da faruwa ne ba tare da kuskure ko tangarda ba.

Duniya tana zagaya rana sau ɗaya a shekara, wato cikin awa 8760, sannan tana juyawa a kan kanta sau ɗaya cikin awa 24, wannan ke kawo dare da rana. Idan da za ka yi tunani sosai, za ka lura cewa wannan tsari ba wai kawai yana faruwa a haɗari ba ne, a’a yana faruwa ne cikin cikakken daidaito da tsari.

Ka duba yadda rana ke bayyana daga gabas kullum, ta yi yamma a ma’auni na hankali, ba tare da wata tangarda ba. Idan da rana za ta fito daga arewa sau ɗaya, ko dare ya daɗe fiye da kima, da komai zai sauya: daga shuka da kiwo har zuwa lafiyar mutane da dabobbi.

Wasu daga cikin tambayoyin da har yanzu kimiyya bata da amsar su: Shin Ina ne iyakar sararin samaniya? Shin duniya ce kaɗai ke ɗauke da rai ko halittu?

Menene a bayan duhun da muke gani a sama? Kimiyya har yanzu ba ta da cikakken amsa ga waɗannan tambayoyi, amma tana ci gaba da buɗe ƙofofi na bincike. Lalle an danganta sararin samaniya da fili mai ci gaba da faɗaɗa kamar iska da ke kumbura a cikin roba. Babu wani abu da ya tabbatar da cewa mu ne kaɗai halittu masu rai, domin akwai miliyoyin taurari da duniyoyi da ke cikin irin tsarin da rana take da shi.

Hakanan, me ke bayan duhun da ke sama har yanzu bai bayyana ba. Amma masana sun ce inda haske ya ƙare, duhu ke farawa, kuma wannan duhu ba komai ba ne illa shiru da nisa da girman fili.

Duniya kamar tana da rai ce: tana numfashi, tana motsi, tana girgiza lokaci-lokaci, tana fitar da aman wuta, tana dumama da kuma sanyaya. Wannan ya nuna mana cewa ba dutse ne kawai ba, jiki ne mai aiki da motsi. Lokacin da girgizar ƙasa ta faru, tana nuna cewa cikin duniya na motsi ne.

Lokacin da aman wuta ya tashi, yana bayyanar da irin zafin da ke cikin jikin ƙasa. Wadannan abubuwa duka suna nuna cewa duniya tana rayuwa da motsi, kuma muna bukatar fahimtar hakan da zurfi.

A rubutu na gaba, zamu sauka daga sararin samaniya mu shiga cikin ƙasa mu binciki me ke ciki, me yasa take girgiza, me ke haddasa aman wuta, da kuma irin zafin da ke ƙasan ƙasa.

About The Author