September 18, 2026

Fagen Kimiyya: Yadda Duniya Ke Numfashi a Cikin Tsari da Hikima a Ƙarƙashin Ƙasa (5)

images - 2025-05-25T180650.253

 

Fagen Kimiyya: Yadda Duniya Ke Numfashi a Cikin Tsari da Hikima a Karkashin Ƙasa (5)

Tare da Abubakar Isah Hassan

Idan muka tsaya naƙalto duniya da kyautata kallon hikimar halittarta, za mu fahimci cewa duniya ba ƙasa ce kawai da muke takawa ba, duniya wata halitta ce mai rai, mai motsi, mai numfashi, wacce kowane motsinta yana da ma’ana. Kamar yadda jikin mutum ya ke da tsarin da ke kula da lafiyarsa, haka duniya ke da tsarin da ke kula da dorewar rayuwa a cikinta.

Ruwa a Matsayin Jinin Duniya

A cikin tsarin duniya, ruwa ba kawai ruwa ba ne. Ruwa shi ne jinin duniya, yana zagayawa daga tekuna zuwa sararin samaniya, daga gajimare zuwa ƙasa, daga ƙasa ya koma rijiyoyi, koguna, da tekuna. Wannan tsarin shine kimiyya ke kira “Hydrological Cycle” kuma yana tafiya ne ta hanyar tururi, haɗuwarsa da sanyi ya zama gajimare, sannan ya sauko a matsayin ruwa.

Amma ba dukkan gajimare ke iya sauke ruwa ba. Sakamakon tasirin yanayi, yanayin zafi da sanyi, da matsin iska suna tsara ko ruwa zai sauka ko a’a. Wannan zai nuna mana cewa duniya na da tsarin kula da kanta ta hanyar ƙa’idojin da Allah ya tsara a matsayin dokokin halittarta, waɗanda masana suke kira da “Laws of thermodynamics da fluid dynamics”.

Kuma yayin da ruwa ke sauka, yana ratsa ƙasa cikin wani tsari da ake kira aquifers, hanyoyin ruwa a ƙasan ƙasa, waɗanda suka yi kama da jijiyoyi da ke ɗaukar jini a jikin ɗan adam. Wannan tsarin tafiyar ruwa yana cikin tsarin kimiyya da ke daidaita zagayen ruwa da samar da ɗanyen albarka, ko kuma ya kawo haɗari idan aka samu gurbacewar yanayi.

Iska a Matsayin Numfashin Duniya

Iska kuwa, shine numfashin duniya. Yana motsawa daga yankunan da rana ke zafafawa sosai wato (high pressure) zuwa wuraren da sanyi ya fi yawa wanda ake kira da (low pressure). Wannan motsin shine ke samar da guguwar iska, hadarin sama, da kuma rahamar da ke kawo sauyi a yanayi. Iska yana tafiya ne tare da wasu sinadarai, yana ɗauko guba ko kuma sabuwar rayuwa irin su Oxygen wanda rayuwarmu ba zata yuwu ba sai da shi.

A wasu lokuta, iska da tururin ruwa su kan haɗu su haifar da guguwa, kamar hurricanes, cyclones, da tornadoes, waɗanda kowa yasan irin abubuwan da suke kawo wa ga rayuwar mu da Muhallin mu.

Binciken kimiyya ya gano yanda iska ya ke motsi yayi kama da yanda huhu ke fitar da iskar carbon dioxide da karɓar iskar oxygen. Wannan yana nuna cewa duniya kamar mutum ce mai rayuwa, mai numfashi, mai motsi kuma tana amsawa kamar yadda jikin mutum ke mayar da martani da ciwo ko lafiya.

Zagayen Rayuwa a Matsayin Hadin Kai Tsakanin Abubuwa

Halittun Mutane, dabbobi, ƙwari, tsirrai da itatuwa ba za su rayu ba tare da ruwa da iska ba. Rayuwa a doron ƙasa ba zai taɓa yiwuwa ba sai tare da wannan haɗin kai na kimiyya. Akwai haɗin kai da ake kira biosphere, wanda ke haɗa tsarin numfashin halittu (respiration), da tsarin photosynthesis, inda tsirrai ke shakar carbon dioxide suna fitar da oxygen, wani nau’i na musayar rai tsakanin duniya da mazaunanta.

Sirrin Ƙasa a Matsayin Wata Hikimar da Ta Boyu

Ba wai kawai duniya ke numfashi a sarari ba ne, har ma a cikin jikinta. A ƙasan duniya akwai tafkuna na wuta wato magma chambers, da suke motsi kamar yanda zuciya ke bugawa. Idan ƙarfin da ke tattare da su ya yi yawa, sai su faso ƙasa su fito, shine muke kira da amon wuta ko volcanoes a turance.

Wannan motsi yana kama da yadda jikin mutum ke amsar zazzabi ko raɗaɗi lokacin da cuta ta shige shi.

Tsarin girgizar ƙasa kuma wato “seismic activity” wani sako ne daga duniya cewa akwai gyara ko tasiri da ke faruwa a cikin jikinta. Wannan yana cikin ilimin geophysics, wanda ke binciken motsin ƙasa da sirrin cikin duniya.

Hikimar Halitta Ta Fuskoki Maban-banta

Zamu lura cewa duniya tana da “hankali” ko da ba a furta ba. Domin Kowane girgiza da motsi, kowane iska, kowane sauyin yanayi yana nuni da wata alama da muke buƙatar karantawa da sa lura.

Kuma wannan yana bayyanar mana da gaskiyar da kimiyya ke neman tabbatarwa: cewa duniya ba kawai wata ƙasa bace mai ɗauke da tsananin sanyi ko zafi kamar yanda wasu suke ɗauka, sai dai mu kalleta a matsayin wata halitta mai homeostasis, wato ikon daidaita kanta, kamar yadda jikin ɗan adam ke daidaita zafin jikinsa.

A rubutunmu na gaba, zamu nutsa cikin zuciyar duwatsu da harshen wuta, mu kalli yanda aman wuta ke tasowa kamar fushin zuciya, da yadda ƙasa ke iya fasa kanta kamar yadda jiki ke amsawa da ciwo.

Za mu fahimci cewa girgizar ƙasa ba wai bala’i ba ce kawai, amma wani sako ne daga halittar da muke zaune a cikinta.

About The Author