Duk Wanda Ya Samu Takara Dole Ya Ajiye Muƙami Idan Yana Da Shi. Cewar Jam’iyyar APC
Katsina Zaɓen 2025: Duk Wanda Ya Samu Takara Dole Ya Ajiye Muƙami Idan Yana Da Shi. Cewar Jam’iyyar AP
Sakataren jam’iyar APC na jihar Katsina kuma shugaban kwamitin sayar fim din takarar Ƙananan hukumomi da Kansiloli Barista Muhammad Namadi ya ja hankalin ‘yan takara da su ajiye makaman su zuwa gobe juma’a
Alhaji Muhammad Namadi ya fadi haka ne a lokacin da yake taron manema labarai a Katsina
A cewar sa, dole a mutunta dokar zaɓe ta 2022 wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya sanya wa hannu.
Ya ce akwai waɗannan suke da muƙaman S.A da wasu mukaman gwamnati, sai dai ya ce shuwagabannin waɗanda suke akan mulki ba sai sun ajiye mukamai ba kamar yadda dokar ta ce.
Haka kuma sakataren jam’iyar APCn ya bada tabbacin cewa ranar 18 ga wannan watan na Mayu za a tabbatar da ‘yan takarar da suka samu nasara ta hanyar sasanci.
“Muna fatan cewa ranar asabar mai zuwa ita ranar da duk ‘yan takara da magoya bayan jam’iyyar APC a faɗin jihar Katsina za su taro a matakin runfuna da mazaɓo domin tabbatar da wannan sasanci’ inji shi
Haka kuma ya yi ƙarin haske akan waɗanda aka ce suna korafi gane da yadda aka fitar da ‘yan takarar ta hanyar sasanci inda ya ce an kama kwamitin da zai saurari korafe-korafe.
Kazalika Barista Muhammad Namadi ya yi bayanin cewa an umarci waɗanda suka samu nasarar yin takara da su nemi waɗanda ba su samu ba domin tattaunawa da su ta fahimtar juna.
Yana mai fatan cewa jam’iyyar su ta APC ita ce zata yi nasara a zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a watan Fabrairun shekarar 2025 mai zuwa indan Allah ya kaimu da rai da lafiya.
