September 18, 2026

Duk Gwamnatin Da Bata San Darajar Ilimi ba, To ya Za a yi Ta Bar ɗan Wani Ya Yi Karatu. Cewar Nura Khalil

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Ɗan Takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar NNPP injiniya Nura Khalil ya bayyana cewa duk wanda bai san darajar ilimi ba, to ba zai bari ‘ya ‘yan wasu su yi karatu ba.

Injiniya Nura Khalil ya fadi haka a wajan wani taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar NNPP da aka gudanar a jiya lahadi a Katsina

Haka kuma ya ƙara da cewa idan aka duba gwamnati da irin mutanen da ke kewaye da ita, babu mamaki idan an jefa yara cikin halin ni ‘ya sun da suke ciki akan harkar ilimi a jihar Katsina.

Sai dai kuma ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar NNPP yana yi wa al’umma albishir da cewa duk abinda Kwankwaso ya aiwatar akan harkar ilimi to shina zai koyi a matakin jiha idan Allah ya ba su nasara.

‘Kamar yadda mai girma Dakta injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wa ‘ yan Najeriya alkawarin cewa ba za su sake biyar kuɗin jarabawa ba, mu ma anan jihar Katsina haka abin zai kasance da yardar Allah” inji shi

Ya ƙara da cewa idan! NNPP ta kafa gwamnati babu batun biyan kudin jarabawa da suka haɗa da WEAC da NECO da kuma Jamb ya ce idan kuma mutum ya zauna Jamb sai ta yi shekaru huɗu yana amfani da Ita.

Injiniya Nura Khalil ya ce matasa dubu saba’in 70,000 da ba su samu damar zauna jarabawar Jamb ba, idan suka samu nasara a zaɓen 2023 gwamnati zata biya ma su kuɗin kyautar Allah.

Da ya juya akan manoma kuwa ɗan takarar gwamnan ya ce rashin tsaro ya maida komi baya a sha’anin noma da kiwo a jihar Katsina saboda ‘yan bindiga sun hana manoma shan ruwa a inuwa

Ya ƙara da cewa wasu manoman sai sun kwaso abinda suka noma sun kawo gida, amma a biyo su har gida ana karɓar haraji kuma gwamnati ta sa ido bata yi komi ba, ya ce zai kawo karshen wannan masifar idan ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar NNPP

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *