September 18, 2026

Da Gaske Ina Neman Kujerar Gwamnan Jihar Katsina a Zaɓen 2023 – Faruk Lawal Joɓe

0

Kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsaran tattalin arziki na jihar Katsina, Alhaji Faruq Lawal Jobe ya tabbatar da batun da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai tsaya takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓe mai zuwa na 2023.

A yau Litinin ne aka wayi gari da labarin cewa kwamshiinan yana cikin masu neman takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar APC a kakar zaɓe mai zuwa.

Wannan labari dai ya sanya alamomin tambaya ga zukatan masoyansa inda suke faɗin cewa da gaske Hon. Jobe zai yi takara, yanzu dai magana ta kare da kansa ya shaidawa kafar Blueink News Hausa cewa lallai yana cikin masu neman wannan kujera.

Hon. Faruq Lawal Jobe kwararren ma’aikacin banki ne dan asalin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina ya ce nan gaba kaɗan zai gudanar da taron manema labarai da zai bayyana manufofinsa da kudurorinsa ga al’ummar jihar Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *