DA DUMI-DUMI: FAAN Ta Gano Gawa A Titin Jirgin Sama Na Lagos.
Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN), ta tabbatar da gano gawa a kan titin jirgin sama mai lamba 18R/36L a ranar Alhamis, inda ta ce an fara bincike kan lamarin.
A wata sanarwar manema labarai da aka ba jaridar LEADERSHIP a jiya Juma’a, babban manajan Kamfanin, Faithful A. Hope-Ivbaze, ya ce an gano gawar mutane da ba a tantance ba a hanyar jirgin saman ranar Alhamis.
