An Rufe Gasar Karatun Al-qur’ani Ta Rabida a Matakin Jiha a Yau Juma’a.
Auwal Isah
Gasar karatun al-qur’anin ta mako daya da ta fara daga ranar Litinin zuwa wannan Juma’ar ta gudana ne a makarantar mata (WTC).
Da yake magana a wurin rufe gasar karatun, kwamishinan ilimi na jihar Katsina ya yaba ma gwamnatin jihar Katsina bisa ba gasar karatun masauki, tare da kashe mata kudi a karkashin ma’aikatar ilimi don ganin ta gudana yadda ya kamata.
Badamasi Lawal Charanchi ya yaba ma wanda aka dama da su cikin gasar, tare da yin kira gare da su roka ma jihar nan dama kasar baki daya zaman lafiya da hadin kai.
Kwashinan ilimin wanda ya samu wakilcin malam Abubakar ya kuma gode ma Allah SWA bisa basu damar gudanar gasar karatun a matakin jihar lafiya lau.
A nashi bangaren, shugaban gasar karatun Mai shara’a Musa Danladi Abubakar ya yi kira ga masu hali da su taimaka wurin yada addinin Muslumci.
Ya kuma roki Allah ya ba wadanda suka samu nasarar lashe gasar karatun a matakin jihar sa’a idan sun je gaba a matakin kasa, tare da yin kira gare su da su linka kwazonsu.
Wadanda suka halarci gasar karatun kuma suka yi jawabi sune: daraktocin makarantu, daraktan gasar karatun a matakin jiha, daraktan tabbatar da ingantaccen ilimi, daraktan Rabida na kasa da kuma jami’ar shirya gasar karatun.
Kuma an tsara gasar karatun ne a matakin izihi daban daban.
A karshen gasar karatun dai, an bada kyautar freezer ga Amina Sa’idu daga shiyyar Funtua da aka dama da ita cikin gasar a matakin izihi 60, sannan kuma aka bada kananan freezer 2, da abun sanwar na gas, da barguna, da zanen gado, da dai sauransu ga wadanda suka zo mataki na 1, dana 2, kuma na 3 a matakin gasar karatun daban daban da bai kai izihi 60 ba.
Kuma daga nan Amina Sa’idu ta karanta wani bangaren na alqur’ani mai girma.
