Cikin Kwana 100: Duk Muƙaman Da Gwamnatin mu Ta Naɗa Bisa Cancanta Ne Cewar Dikko Raɗɗa
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ƙara jaddada cewa duk abinda yake a gwamnatin sa musamman naɗa muƙaman siyasa yana yin su ne bisa cancanta, ba san rai ba.
Gwamnan wanda ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa al’ummar jihar Katsina bayanin irin abubuwan ya yi a cikin kwana 100 da fara wannan gwamnati ta sa.
Wannan Bayani ya biyo bayan wata tambaya da aka yi masa akan sa-tuka-sa-katsi da ke faruwa a hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Katsina inda aka naɗa Farfesa Sani Mashi a matsayin shugaba.
Jama’a da dama na kallon gwamna Malam Dikko Raɗɗa a matsayin wanda ya yi wa dokar hukumar karan tsaye, inda dokar hukumar ta ce duk wanda zai shugabanci Hukumar dole ya zama masanin tattalin arziki ko kuma harkokin kuɗaɗen, amma sai gashi an naɗa Farfesar masani yanayi da taswira
Malam Dikko Raɗɗa ya ce duk muƙaman da yake naɗawa a gwamnatin sa babu inda ya saɓa ƙa’ida ko alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Kazalika ya ƙara tabbatarwa da duniya cewa yana nan akan matsayin sa na fatatakar ‘yan bindiga ba tare da yin sulhu da su ba, sai dai ya ƙara da cewa duk ɗan bindigar da ya ajiye makaminsa ya zo domin zaman lafiya zai karɓe shi cikin amince.
Gwamnan wanda ya ce bai ɗauki yin bikin kwana 100 da hawan gwamnati sa a matsayin wani babban abu, sai dai ya ce akwai bukatar yi wa mutanen jihar Katsina bayanin halin da gwamnatin sa take ciki saboda ya ɗauki alƙawari tun farko.
“Abinda da ke da mahimmanci shi ne, a duba irin rawar da muka taka a cikin wannan ƙanƙanin lokaci sannan tuni mun fara yin abubuwan da suka da ce wanda kuma muka yi wa al’umma alƙawari” inji Dikko Raɗɗa.
