Buhari Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Ɗan Takarar Sanata Na jam’iyyar Labour, Oyibo Chukwu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan gillar da aka yi wa dan takarar kujerar Sanatan Enugu ta Gabas na Jam’iyyar Labour, Oyibo Chukwu da mai taimaka masa.
Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai, Femi Adesina, ya yi amannar wadanda suka aikata wannan ta’asa a Awkunanaw, karamar hukumar Enugu ta Kudu a Jihar Enugu, ba su mutunta rai da mutuncin dan Adam, don haka sun cancanci su gamu da aikin doka.
Shugaban ya tabbatar da kudurin sa na gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Thisdaylive.
