Mutane 15 Sun Mutu, 7 Sun Jikkata A wani Hatsarin Mota A Bauchi.
Akalla mutane 15 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu 7 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a babbar hanyar Jos zuwa Bauchi.
Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi a rahoton farko da ta fitar game da hatsarin, ta ce ya faru ne tsakanin wata babbar mota da wata motar safa.
Hukumar ta ci gaba da cewa, hadarin ya afku ne a unguwar Nabordo da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos da tirela mai lamba DKD32 XB, da wata motar bas kirar Toyota Hiace mai lamba YLA 984XA.
Rahotanni sun bayyana cewa motar ta Dangote ce, yayin da motar Toyotar ta kamfanin sufurin jiragen sama na Sunshine na jihar Adamawa ce.
“A dunkule mutane 22 ne hatsarin ya rutsa da su da suka haɗa da Mata 2, Maza 18, yarinya 1 da yaro 1.
Rahoton na hukumar kiyaye haɗurran ya kara da cewa “Mutane 15 ne suka mutu wanda ya ƙunshi maza manya 12, babbar mace 1, yaro 1 da yarinya 1, yayin da wadanda suka samu raunuka 7 suka haɗa da manyan maza 6 da babbar mace 1.”, Kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership ta bayyana.
